Kaza

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kaza
Scientific classification
KingdomAnimalia
PhylumChordata
ClassAves
OrderGalliformes (en) Galliformes
DangiPhasianidae (en) Phasianidae
GenusGallus (en) Gallus
subspecies (en) Fassara Gallus gallus domesticus
,
General information
Tsatso chicken breast (en) Fassara, chicken meat (en) Fassara da chicken egg (en) Fassara
Kimanin bugun zuciya 275 beats per minute (en) Fassara
jariran kaji
kaza a tsaye

Kaza wata tsuntsuwa ce na daga cikin jinsin tsuntsaye waɗanda ake ajiyewa a gida domin kiwo. Mutane nayin kiwon kaji ne domin amfana da naman su ko kuma kwansu ko kuma don a sayar domin kuɗi. Kaza tana yin kwanta dakanta kuma ta kyankyashe kayanta ba kamar wasu nau'in tsuntsaye ba, da basa iya kyankyashe kwansu. Namijin kaza shi ne ake kira da zakara mace kuma ana kiranta da kaza. Akwai kazar Hausa da kuma kazar Bature wadda inji yake ƙyanƙyashe su. Sannan akwai kazar Fulani irin wacce Fulani suke kiyo, girman kajin Fulani ya banbanta da sauran kaji, saboda yadda Fulani suke kiwon nasu. Har ila yau kaza dai nama ce mai farin jini wajen mutane saboda naman kaza ya banbanta da sauran namann tsinsaye. Naman kaza yana ɗaya daga cikin naman da aka fi ci a duniya.

Ita kaza tanada baiwar ƙyanƙyashe kwayayenta, amma wasu halittun tsuntsaye irin su zabbi da talatalo har da Agwagwa takan ƙyanƙyashe kwansu idan an sanya mata. Har ila yau kaza tana kan gaba acikin tsuntsaye da aka fi siya a duniya, kuma da aka fi ci, saboda dadinta da kuma wasu sinadarai da yake tattare da ita.

Zakara.
Wani jinsi na kazar gidan gona.
Kaza da ƴaƴanta.
Zakara yana yin cara.

Rabe-raben kaloli na kaji[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai kala kala a cikin jinsin kaji, kamar baka da fara da ja, sai kuma masu hade da kaloli kamar mai ja da baki dama wani ratsi na fari ko shudi, ko kuma mai digo na fari da baki a dukkan jikinta. Akwai kuma nau'in kaza da ake kira nama wuya wanda zaka gansu babu gashi a wuyan su.

Wake waken kaza.

Kalli hotunan Kaji[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]