Abatete Gari ne a Jihar Anambra a Najeriya.[1] Abatete ya yi iyaka da garuruwan; Uke, Ogidi, Abacha, Oraukwu, Alor, Ideani, Nimo, Eziowelle, Umuoji. Garin na cikin ƙaramar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra. Garin ya ƙunshi ƙauyuka huɗu ne : Agbaja, Nsukwu, Ogbu and Odida. Mutanen garin na ɗaya daga cikin al'ummar Gabashin Najeriya masu magana da harshen Igbo. Abatete, kamar yawancin al'ummomin Igbo, suna da kyawawan al'adun gargajiya.
[2]