Abba Ibrahim Garko

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Abba Ibrahim Garko (An haife shi ranar 1 ga Agusta, 1963), a garin Garko. Ɗan siyasa ne.

Farkon rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Ya yi makarantar firamare ta Garko (1971 – 1978). Sannan ya halarci makarantar sakandaren kasuwanci ta Wudil tsakanin 1978 – 1983. Hon. Ya yi aiki a matsayin Auditor da Gwamnatin Jihar Kano. Ya yi ritaya da radin kansa ya shiga harkokin siyasa a shekarar 2007. [1]

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

An zabe shi mataimakin shugaban jam’iyyar All People’s Party (ANPP) 2007 – 2010. Ya kuma rike mukamin Karamar Hukumar Mulki Sole (Takai Local Government). An zabi Honorabul Garko a matsayin dan majalisar jiha sau biyu. A halin yanzu shi ne shugaban kwamitin majalisar kan harkokin kananan hukumomi. [2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]