Abincin gargajiya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Abincin gargajiya Abincinmu na gargajiya yana da matukar alfanun gaske fiye da na yanzu, domin kuwa yana ɗauke da sinadarai masu kara yawaitar jini, bunkasa karfin garkuwar jiki, kuma masu samar da karfin qassa ga jiki, masu gina jiki, sauwake kumburin ciki da dai sauransu.

Ire-Iren Abincin Gargajiya[gyara sashe | gyara masomin]

1-Tuwon dawa : dawa tana samarda karfi sosai ga jikin mutum, tana sa mutum idan yaci baya jin cikinsa ya kumbure, kuma bata haifar da taurin bayan gari (hard stool). mai cin tuwon dawa zaiga bayan garinsa da laushi ba ciwo ko wahalar fita.

2.Tuwon masara : dukda yake akwai waɗanda suka camfa masara da wai tana shan jini kuma bata da amfani wanda wannan labarine kawai na rashin tushe balle makama. Tuwon Masara na saurin narkewa a cikin kankanin lokaci kuma bata kabe ciki, mai neman yawan cin abinci to ya fake cin tuwon masara (stimulates appetite) mai kashi kamar na dabbobi shi ma ya rinka cin tuwon masara.

3.Gero : da turanci (millet) kusan gero yakasance abincin da ake iya sarrafawa daban daban kama daga ayi tuwonsa, ayi fura da shi, ayi gumba, ayi kununsa, ayi masa ko waina da shi, ayi garinsa a maida shi dambu, da sauran nau’in abinci. Kuma duka zai bada wata fa’ida dake amfanar jiki.shi ma dai Carbohydrate ne a don haka sai a ci dan a samarwa jiki da karfi.

4-Alkama : ɗaukacin mutane basu san amfanin alkama ba, wasu ko ganinta basu taɓa yi ba. Akwai rubutu na musamman akan fa’idodin alkama da zan kawo maku da kuma dinbin maganin da take yi.

5.Nono : A yau mutanen sun fi son su sayi yoghurt su sha bisa ga nonon shanun da muka gado tun fil azal, wata damuwa anan ma shine akwai yoghurt dinda kamar garin masarane ake gyarawa a zubowa suga a zo ana sayar muna,yau dai ga yoghurt nan kowace iri gani kake ga tsabar zaqi tare da ita.Amma shi nono idan ka same shi kamar kindirmo to sai ka burkake ka sha,zaka ji jikinka da qwaqwalwarka dama cikinka da wani sauyi na daban,kuma zaka ga yanda jikinka zai canza.

6.Dussar gero idan an surfe aka cire dussar to idan so samune a dake dussar a mai data kamar gumba sai a jefa kanwar tuwo a dama a sha.A hakika tana gina jiki tana inganta lafiyar jiki, tana kara karfin immunity, tana yashe cutukkan ciki ta sauwaqe wahalar bayan gari. bugu da kari kuma tana sa kaji kana son cin abinci.[1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-06-19. Retrieved 2022-06-16.