Abubakar Atiku ɗan Shehu Usman

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Abubakar Atiku ɗan Shehu Usman (1837-1847) shine ɗa na huɗu a cikin yaran mujaddadi shehu Usman Dan Fodiyo. An haife shi a Dagel a shekarar 1784 kuma shine ƙani ne ga Muhammadu Bello. Hakan Mahaifiyarsa itace Hauwau Bint Mu'allim Adam, ta uku daga cikin matan shehu Dan fodio.

Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

Mahaifiyarshi ta fara koyar dashi kamar yadda yake a al'adar gidan su. Daganan mahaifin shi da kuma kawon shi mallam Abdullahi da kuma malamai dake cikin dagel. Atiku ya fara ne da karatun 'Allo' daga nan ya cigaba da neman ilimi.

Sarauta[gyara sashe | gyara masomin]

Tun karkashin yayan shi, duba da dabi'un sa. Bello ya nada shi ya kula da Gandi da kuma Bakura. An nada atiku kwana bakwai da mutuwar sarki Bello wannan ya biyo bayane bisa ga dokan da khalifa bello ya sanya da kanshi.Khalifa atiku ya amshi shugabanci bayan rasuwar Sarki Bello a 25 ga watan octoban shekarar 1837, a Masallacin Wurno.

Rasuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Khalifa ya rasu a garin Katuru a jihar Zamfara na yanzu. A hanyar shi ta zuwa Sokoto bayan yarjejeniya da Gobirawa, Abzenawa da kuma katsinawa a watan nuwanban shekarar 1842. ya kuma rasu yana da shekara 60.

Bibiliyo[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]