Abubakar D. Aliyu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Abubakar D Aliyu (An haife shi a shekarar 1966) a garin potiskum.[1]

Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

Abubakar D Aliyu ya halarci makarantar Jimeta Central Primary, a shekarar 1979. Ya wuce GSSS Monguno a jihar Borno inda ya kammala karatunsa a shekarar 1984. Daga baya Aliyu ya wuce Kaduna State Polytechnic inda ya kammala difloma (ND) a fannin Injiniya a shekarar 1988 da HND a High Ways and Transportation Engineering a 1993.[2] A shekarar 1999 ya samu digirinsa na farko a fannin Injiniya a fannin Albarkatun Ruwa a Jami'ar Maiduguri. A halin yanzu ya kasance Fellow a Nigerian Society of Engineers.

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Abubakar ya yi aiki a matsayin jami'in fasaha a ma'aikatar ayyuka ta jahar Bornoa shekarar 1988 zuwa 1991, ya zama babban injiniyan injiniyoyi sannan kuma shugaban sashen engineering a shekarar 2004, da kuma Supervising Project Engineers Yobe State Ministry of Housing a 2007. Aliyu ya kuma kasance Manajan Darakta na Hukumar Kula da Gidaje da Kaddarori ta Jahar Yobea shekarar 2009, mai kula da ma’aikatar lafiya ta Jahar Yobe, da kuma mai kula da ma’aikatar kasuwanci ta Jihar Yobe. Ya kasance mai kula da ma'aikatar hadin gwiwar raya karkara ta jihar Yobe.[3]

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Mataimakin Gwamna[gyara sashe | gyara masomin]

Yayi mataimakin gwamnan jihar Yobe tun daga shekarar 2009 har izuwa shekarar 2019.

Minista[gyara sashe | gyara masomin]

Shugaba Muhammadu Buhari Ya naɗa shi Ministan Ayyuka da Gidaje a shekarar 2019.[4]

Shugabancin Kungiya[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Shugaban Qungiyar Task Force ta Jiha akan rigakafi da kiwon lafiya.
  2. Shugaban Kwamitin Jiha Kan Matsugunni Da Gyaran Matsugunan 'Yan Gudun Hijira
  3. Shugaban Kwamitin kan iyaka na Jiha
  4. Shugaban Kwamitin Tsaftar mahalli na Jiha.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-12-03. Retrieved 2021-12-03.
  2. https://www.blueprint.ng/my-secret-as-longest-serving-deputy-governor/engr-abubakar-d-aliyu-yobe-state-deputy-governor/ Archived 2021-12-03 at the Wayback Machine
  3. https://www.premiumtimesng.com/news/top-news/493121-power-minister-unable-to-defend-n42bn-project-in-2022-budget-before-senate.html
  4. https://www.thisdaylive.com/index.php/2020/11/25/whats-the-minister-of-state-for-works-doing/