Abubakar Sulaiman

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abubakar Sulaiman
Rayuwa
Sana'a

Farfesa Abubakar Olanrewaju Sulaiman jami'in ilimi ne kuma jami'in gwamnati a Najeriya.[1] Shi ne Darakta Janar na yanzu a Cibiyar Nazarin Dokoki da Dimokuradiyya ta Ƙasa.[2] Ya kasance tsohon Ministan Tsare-tsare na Tarayyar Najeriya daga watan Yuli 2014 zuwa Mayu 2015.[3]


Ilimi da aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Sulaiman ɗan jihar Kwara ne a Najeriya. A shekarar 1990, ya kammala karatu daga Jami’ar Ahmadu Bello da digiri a fannin kimiyyar siyasa. A shekarar 1995, ya samu digirin sa na biyu a fannin hulɗar ƙasa da ƙasa da kuma nazarin dabarun bincike a jami'ar Jos. Ya samu Ph.D. Ya karanta International Relations a Jami’ar Abuja a shekara ta 2003.[4] An ba shi Certificate a Jagorancin Jama'a daga Makarantar Gwamnati ta Harvard Kennedy a cikin watan Janairu 2023.[5] Ya shafe shekaru sama da 20 yana karantarwa da bincike, Farfesa ne a Kimiyyar Siyasa a Jami'ar Abuja.[6][7]

A shekarar 2019, an naɗa Sulaiman Darakta Janar a Cibiyar Nazarin Majalisun Dokoki da Dimokuraɗiyya ta Ƙasa. An sake naɗa shi a watan Afrilu 2023 na wani wa'adin shekaru hudu.[8] He was reappointed in April 2023 for another four-year tenure.[9]

Ra'ayoyin Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 2015, Sulaiman, a cikin ofishin ministan tsare-tsare na ƙasa, ya zargi gwamnatin jihar Kwara ta lokacin da cin hanci da rashawa, bayan da ya dage kan hanyoyin da ake ba da kwangilolin ba su dace ba.[10] A watan Nuwamban 2017, Sulalman ya soki gwamnatin Buhari kan kashe ‘yan Biafra 400, da 'yan Harkar Musulunci a Najeriya da aka kashe a lokacin mulkinsa.[11]


Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Nwogu, Success (2019-09-29). "Nobody thought I'd become a professor – Prof. Abubakar Sulaiman". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2023-06-23.
  2. Rapheal (2023-04-20). "Extraordinary Prof. Sulaiman getting encore at NILDS". The Sun Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-06-23.
  3. Admin. "Cabinet Ministers". Budget and National Planning Arm (in Turanci). Retrieved 2023-06-23.
  4. Shola, Shittu (2019-06-03). "Saraki appoints Prof. Abubakar Suleiman as DG NILDS". Daily Nigerian (in Turanci). Archived from the original on 2023-06-25. Retrieved 2023-06-23.
  5. "Ex-minister, Sulaiman, Awarded Harvard Executive Certificate in Public Leadership - THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com (in Turanci). Retrieved 2023-06-23.
  6. Joke (2023-05-04). "Profile of the Director-General, NILDS, Prof. Abubakar O. Sulaiman". NILDS (in Turanci). Retrieved 2023-06-23.
  7. Newspapers, Blueprint (2018-12-21). "Kwara 2019: We won't surrender our sovereignty – Prof Suleiman". Blueprint Newspapers (in Turanci). Retrieved 2023-06-23.
  8. "Saraki appoints Prof. Abubakar Suleiman as DG NILDS - Daily Trust". dailytrust.com. 3 June 2019. Retrieved 2023-06-23.
  9. https://thenationonlineng.net/former-minister-suleiman-reappointed-nilds-dg/
  10. Television, Channels (2015-02-25). "National Planning Minister Accuses Kwara State Government of Currupt Practices". www.channelstv.com. Retrieved 2023-06-25.
  11. Nwachukwu, John Owen (2017-11-08). "Biafra: Buhari must account for killing IPOB members - Ex-minister, Abubakar Sulaiman". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-06-25.