Adamu Ncahama Baba-Kutigi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Adamu Ncahama Baba-Kutigi
Rayuwa
Haihuwa 10 ga Yuni, 1956 (67 shekaru)
Sana'a
Imani
Addini Musulunci

Farfesa Adamu Ncahma Baba-Kutigi ( An haifeshi ranar 10 ga watan Yunin shekarar 1956), a Kutigi, ƙaramar hukumar Lavun, a jihar Neja. Ya kasance tsohon shugaban riƙo na jami'ar tarayya ta Dutsinma.

Rayuwar farko[gyara sashe | gyara masomin]

An kuma haifi Baba-Kutigi ranar 10 ga Yuni 1956 a Kutigi ga dangin Nupe. Ya yi karatun firamare a Sakandaren Gwamnati Eyagi, Bida, Jihar Neja. Ya samu takardar shedar karatun sa ta Najeriya (NCE) a kwalejin horar da malamai ta Minna wadda a yanzu ake kira da, Kwalejin ilimi ta Minna, a shekarar 1979. Ya kuma halarci tsohuwar jami'ar Sokoto, yanzu haka Jami'ar Usman Danfodio, inda kuma daga nan ya samu digiri na farko a fannin kimiyyar lissafi sannan ya sami digiri na biyu a fannin kimiyyar lissafi daga ABU Zaria.

Yana da kuma gogewa wajen koyarwa da bincike, kuma memba ne a ƙungiyar Malaman Kimiyya ta Najeriya (STAN), Cibiyar Nazarin Kimiyya ta Najeriya (NIP) da kuma a ƙungiyar Malaman Fasaha ta Najeriya (NATT). Ya yi aiki a matsayin Mataimakin Darakta, Cibiyar Nazarin Farko da Ƙarfafa ɗabi'a kuma a matsayin memba a Majalisar Mulki mai wakiltar Ikilisiya a Jami'ar Fasaha ta Tarayya ta Minna. [1]

A matsayin Mataimakin Shugaban Jami'ar[gyara sashe | gyara masomin]

Majalisar gudanarwar Jami’ar Tarayya ta Dutsinma, Katsina, ta kuma amince da naɗin Farfesa Adamu Nchama Baba-Kutigi a matsayin sabon mataimakin shugaban jami’ar. Hakan ya biyo bayan naɗin da majalisar dattawan da jami’ar ta yi a taron gaggawa karo na 73 da aka gudanar a watan Maris ɗin shekarar 2019. Kafin naɗin, Prof. Nchama Baba-Kutigi ya kasance tsohon shugaban tsangayar kimiyya na nan take, kuma shi ne tsohon shugaban sashen nazarin kimiyyar lissafi a jami’ar. [2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Baba-Kutigi "Baba-Kutigi the new VC Fudma. retrieved 26 June 2019. Independent
  2. FUDMA News "Federal University Dutsinma get acting vice chancellor" Archived 2019-06-26 at the Wayback Machine retrieved 26 June 2019. Daily Trust