Audu Bako

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Audu Bako
gwamnan jihar Kano

Mayu 1967 - ga Yuli, 1975 - Sani Bello
Rayuwa
Haihuwa Kaduna, 24 Nuwamba, 1924
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Mutuwa 1980
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da Manoma

Audu Bako Tsohon kwamishinan yan sanda ne Mai ritaya, an kuma haife shi a shekara ta alif 1924, Shine gwamnan farko na jihar Kano, Nijeriya a lokacin mulkin soja na General Yakubu Gowon bayan kafuwar jahar daga yankin Arewacin Najeriya.

Tarihin sa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Audu Bako a shekarar 1924 a Barikin yan sanda dake Kaduna. Mahaifinsa yayi aikin dan sanda na tsawon shekaru 36. Audu yayi karatu a Makarantar Kaduna Government School da kuma Zariya Middle School. Bako ya shiga aikin dansanda a 1942. [1]

Gwamnan Jihar Kano[gyara sashe | gyara masomin]

An kuma naɗa shi a matsayin Gwamnan Jihar Kano a lokacin tshohuwar jahar ta Kano a shekarar 1967 lokacin mulkin soja. Bako yayi aiyukan raya kasa sosai a jahar ta kano. A shekarar 1969 ya fara gina madatsar ruwa ta Bagauda. Tsakanin 1970-1973 gwamnatinsa ta gina babbar madatsar ruwa ta Tiga, domib bunkasa harkar Noma. Aikinsa na samar da ruwansha na Timas Danbatta ya tsaya, har sai a shekarar 2008 sannan aka karasa shi inda ake samar da ruwan sha ga kananan hukumomin Dambatta, Makoda da Minjibir.

Rayuwar sa[gyara sashe | gyara masomin]

Audu Bako yayi ritaya a shekarar 1975 lokacin mulkin retired a shekarar 1975 Murtala Muhammed inda ya kama aikin noma a jahar Sokoto. Ya rasu a shekarar 1980 yabar mata da yaya 11. Bayan rasuwar sa an sauya ma matsar ruwa ta tiga zuwa sunan [2] Audu bako yasha samun kyaututtuka a wasannin kwallon doki (wato Polo). Ana matukar girmama Audu Bako sosai.[3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. John N. Paden, Religion and political culture in Kano, University of California Press, 1973, ISBN: 0-520-01738-2, p. 339.
  2. Raph Uwechue, Africa who's who, Volume 1, Africa Journal Ltd. for Africa Books Ltd., 1981, ISBN: 0-903274-14-0, p. 71.
  3. Beverly Blow Mack, Muslim women sing: Hausa popular song, Indiana University Press, 2004, ISBN: 0-253-21729-6, p. 66.