Bikin Rigata

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Bikin Al'adun Gargajiya na Rigata wanda yake gudana a duk shekara a Jihar Kebbi, a ƙaramar hukumar Yauri. Wanda Masarautar Yauri ita take gudanar da bikin, kuma ita ke ɗaukar nauyinshi.[1]

Tarihi Rigata[gyara sashe | gyara masomin]

Kalmar Rigata ta samo asali ne daga yaren Gungawa, wadda kalmar tana nufin "Yaƙin ruwa". A lokacin bikin ana wasannin motsa jikin koguna da wasan ruwa. An fara wannan bikin shekaru 200 da suka shuɗe, wanda bikin yana nuni da ƙarfin sojojin ruwa na sojojin Gungu, Inda mayaƙan Gungu suka kai hari a kan kogin Neja wanda a lokacin ake kallo yanada hatsarin gaske, mayaƙan suna hawan kwale-kwale masu girma daban-daban gami da makamai daban-daban domin kai farmaki kan wasu mayaƙan da ke cikin ruwan. Wannan al'adar itace a matsayin atisayen horar da mayaƙan Gungu masu zuwa. Sai dai bikin ya samu tangarɗa a lokacin zuwan turawan mulkin mallaka, don sun hana kama nau'in kadar dake cikin ruwan, don gudun kada nau'in ta ɓace a kogin. Al'adar wadda Sarkin Yauri na 42 ya ƙara jadadda ta.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Ajoge, Ayodele (1 February 2024). "Yauri Emirate set to hold Rigata cultural festival". tribuneonlineng.com (in Turanci). Retrieved 14 February 2024.