Chisinau ko Cisinu[1] (da harshen Maldoba: Chișinău) birni ne, da ke a ƙasar Maldoba. Shi ne babban birnin ƙasar Maldoba. Chisinau yana da yawan jama'a 532,513 bisa ga jimillar 2014. An gina birnin Chisinau a karni na sha biyar bayan haifuwar Annabi Issa. Shugaban birnin Chisinau Ion Ceban ne.