Daular Qajar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Daular Qajar
دولت عَلیّهٔ ایران (fa)
Babbar kasar Iran
ممالک محروسهٔ ایران (fa)
Masarautu masu tsaro Iran
Tuta (1906-1925) Makamashi (1907-1925)
Tuta (1906-1925) Makamashi (1907-1925)

Taswirar Iran karkashin daular Qajar a karni na 19

Take (1873–1909)
Salâm-e Shâh
(Sallamar sarauta)

(1909–1925)
Salamati-ye Dowlat-e 'Aliyye-ye Iran
(Gaisuwa ga babbar kasar Iran)

Wuri
Map
 35°42′00″N 51°25′00″E / 35.7°N 51.4166669°E / 35.7; 51.4166669
Shah
  • Agha Mohammad Khan Qajar (farko)
  • Ahmad Shah Qajar (karshe)
Vazir-e A'zam
  • Hajji Ibrahim Shirazi (farko)
  • Mirza Nasrullah Khan (karshe)
  • Firayam Minista
  • Sultan Ali Wazir Afkham (farko)
  • Reza Pahlavi (karshe)

  • Babban birni Tehran
    Yawan mutane
    Harshen gwamnati Farisawa (wallafe-wallafen kotu / harshe, gudanarwa, al'adu, hukuma)
    Azerbaijani (harshen kotu da harshen uwa na gidan sarauta)
    Addini Shi'a
    Bayanan tarihi
    Mabiyi Daular Zand
    Daular Afsharid
    Daular Durrani
    Khanatu na Kalat
    Masarautar Kartli-Kheti
    Ƙirƙira 1785
    Rushewa 1925
    Ta biyo baya Daular Pahlavi
    Daular Rasha
    Masarautar Afghanistan
    Tsarin Siyasa
    Tsarin gwamnati Cikakken sarauta (1789–1906)
    tsarin mulki sarauta (1906–1925)
    Gangar majalisa Majalisar Shura ta kasa (1906–1925)
    Ikonomi
    Kuɗi Iranian toman (en) Fassara

    Qajar Iran (Farisawa ايران قاجارى Irân Qājāri) ana kuma kiranta da Qajar Farisa[1] (Farisawa فارس قاجارى Faris Qājāri), Daular Qajar (Farisawa شاهنشاهى قاجار Šāhanšāhi-ye Qājār), bisa hukuma Maɗaukakin Ƙasar Farisa (Farisawa دولت عَلیّهٔ ایران Dowlat-e 'Aliyye-ye Irân) kuma ana kiranta da Masarautu masu tsaro Iran (Farisawa ممالک محروسهٔ ایران Mamâlek-e Mahruse-ye Irân[2]) kasa ce ta Iran[3] wacce daular Qajar ta mulki daga 1789 zuwa 1925. Iyalan Qajar sun mamaye Iran gaba daya a shekara ta 1794, inda suka kori Lotf 'Ali Khan, Shah na karshe na daular Zand kuma suka sake tabbatar da ikon Iran akan manyan sassan Caucasus. A cikin 1796, Agha Mohammad Khan Qajar ya ƙwace Mashhad cikin sauƙi,[4] wanda ya kawo ƙarshen daular Afsharid. Iran ta hade kuma aka ayyana Agha Muhammad Khan Qajar shah na daular.[5]

    Daga baya juyin juya halin tsarin mulki ya faru. Bayan juyin mulkin da aka yi a zamanin mulkin Muzaffar al-Din Shah, sarki mai jiran gado Muhammad Ali Shah ya yi adawa da shi tare da rufe majalisar. Rikicin cikin gida da waje ya haifar da tashin hankali a kasar, kuma sarkin Qajar na karshe shi ne Ahmad Shah Qajar wanda aka hambarar da shi a shekara ta 1925 kuma Reza Pahlavi ya zama Shah na Iran.[6]

    Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

    1. Qajar Persia.
    2. History of Persia.
    3. Abbas Amanat, The Pivot of the Universe: Nasir Al-Din Shah Qajar and the Iranian Monarchy, 1831–1896, I. B. Tauris, pp 2–3
    4. H. Scheel; Jaschke, Gerhard; H. Braun; Spuler, Bertold; T. Koszinowski; Bagley, Frank (1981).
    5. Iran : History.
    6. Qajar.