Isah Chiroma

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Isah Chiroma
director general (en) Fassara

ga Faburairu, 2018 -
Rayuwa
Haihuwa Mubi, 13 ga Afirilu, 1963 (61 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Maiduguri
Jami'ar Jos
Matakin karatu Bachelor of Laws (en) Fassara
Master of Laws (en) Fassara
doctorate (en) Fassara
Sana'a
Sana'a Lauya da university teacher (en) Fassara

Isa Hayatu Chiroma an haife shi a ranar (13 ga watan Afrilu shekara ta 1963) masanin shari'a ne a Najeriya kuma farfesa a fannin shari'a a Jami'ar Maiduguri. A watan Fabrairu shekara ta 2018, Muhammadu Buhari ya naɗa shi a matsayin Darakta Janar na Makarantar Shari'a ta Najeriya.[1][2] Ya maye gurbin Farfesa Olanrewaju Onadeko wanda ya yi shekara takwas.[3] Kafin nada shi, ya kasance mataimakin darakta a makarantar Yola campus of Nigeria Law School daga shekarar 2011 zuwa 2016.[4][5] Ya zama Babban Lauyan Najeriya, (SAN) wanda aka zaɓa a taron zama na 133 a cikin shekara ta 2018.[6]

Tasowar sa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Isa Hayatu a garin Mubi dake ƙaramar hukumar Mubi ta Arewa a jihar Adamawa.[7] Ya fara makarantar farko a shekarar 1970 a Mubi Primary School zuwa 1976 sannan ya wuce makarantar sakandare a Government Technical School Mubi a shekarar 1976 zuwa 1981. Ya samu digirin sa na farko a fannin shari'a a shekarar 1986, ya kuma yi digiri na biyu a fannin shari'a a shekarar 1991 a Jami'ar Maiduguri, sannan ya yi digirin digirgir (PhD). Inda ya sake karanta fannin Shari'a a 2005 a Jami'ar Jos.[8]

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Ya fara aiki a matsayin mataimakin lakcara (assistant lecturer) a tsangayar shari'a a jami'ar Maiduguri a shekarar 1988 yana koyar da darussan administrative, constitutional, Islamic, policy and Human law, environmental law and Islamic jurisprudence courses a shekarar da aka kira shi da matsayin Bar daga nan har lokacin da ya zama farfesa a fannin shari'a a shekarar 2005. Ya yi aiki a matsayin shugaban tsangaya ta kowa da kowa, Shari'a, shugaban Shari'a kuma shugaba a Consultancy Services Centre a jami'ar Maiduguri. Ya kafa da kuma daidaita shirin Clinical Legal Education Program kuma ya zama memba a Majalisar Dattawan Jami'ar, kuma memba ne a Legal Practitioners, Privileges Committee for Selection of Senior Advocate of Nigeria a Akadamiyya kuma memba ne mai shugabantar Governing Council of Federal Polytechnic Mubi, jihar Adamawa. Amma Fanni na musamman da yafi kwarewa shine Environmental Law and Policy, Humanitarian Law, Human Rights, Access to Justice, Law and Development and Ethics in the teaching and practice of Law. Chiroma ya kula da bincike da yawa dangane da yankin da yake sha'awa kuma memba ne a African Law Association of Germany, Global Alliance for Justice Education, International Bar Association, Nigerian Institute of Mediators and Conciliators, Nigerian Bar Association, Society for Corporate Governance and Fellow of the Chartered Institute of Arbitrators, Notary Public person.[9]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Buhari appoints heads for Sovereign Wealth Fund, Nigerian Law School | Premium Times Nigeria" (in Turanci). 2017-10-12. Retrieved 2020-10-06.
  2. "Buhari re-appoints Orji as MD Sovereign Fund, appoints new DG for Law School -". The Eagle Online (in Turanci). 2017-10-13. Retrieved 2020-10-06.
  3. Ifeoma, Peters. "Prof. Isa Hayatu Chiroma Assumes Office as New DG, Nigerian Law School". DNL Legal and Style (in Turanci). Archived from the original on 2020-10-09. Retrieved 2020-10-06.
  4. "New DG for Nigerian Law emerges – YOUTHSNG" (in Turanci). Retrieved 2020-10-06.[permanent dead link]
  5. BusinessDay (2018-04-04). "Prof Isa Chiroma as DG Nigerian Law School rekindles hope in future of legal profession". Businessday NG (in Turanci). Retrieved 2020-10-06.
  6. "DG law school Prof Isa Hayatu Chiroma Prof Mohammed Mustapha Akanbi and 29 lawyers elevated to SAN". thenigerialawyer.com. Retrieved 2020-10-06.
  7. "Prof. Isa Hayatu Chiroma: Profile of Nigerian Law School DG". myNAIJAinfo (in Turanci). 2017-10-13. Archived from the original on 2020-10-08. Retrieved 2020-10-06.
  8. Reporter, Our (2020-07-08). "Prof. Isa Hayatu Chiroma (DG, Council of Legal Education)". Nigerian Pilot News (in Turanci). Retrieved 2020-10-06.
  9. "About Nigerian Law School". www.nigerianlawschool.edu.ng. Archived from the original on 2018-10-13. Retrieved 2020-10-06.