Jimin

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jimin
Rayuwa
Cikakken suna 박지민
Haihuwa Busan, 13 Oktoba 1995 (28 shekaru)
ƙasa Koriya ta Kudu
Karatu
Makaranta Global Cyber University (en) Fassara
Harsuna Korean (en) Fassara
Sana'a
Sana'a mawaƙi, mai rawa da mai rubuta waka
Tsayi 175 cm
Mamba BTS
Sunan mahaifi Jimin
Artistic movement K-pop (en) Fassara
Yanayin murya countertenor (en) Fassara
Kayan kida murya
Jadawalin Kiɗa HYBE (en) Fassara
IMDb nm8062274
ibighit.com…

Park Ji-min (Yaren mutanen Koriya: 박지민; an haifeshi Oktoba 13, 1995), wanda aka sani da suna Jimin, mawakin Koriya ta Kudu ne, marubuci kuma dan rawa. A cikin 2013, ya fara fitowa a matsayin memba na kungiyar saurayin Koriya ta Kudu BTS, karkashin lakabin rikodin na Big Hit Entertainment. Jimin ya fito da wakokin solo guda uku a karkashin group na BTS-"Lie" a cikin 2016, "Serendipity" a cikin 2017, da "Filter" a cikin 2020-duk wadanda suka hau akan Chart Digital Gaon na Koriya ta Kudu. Ya fito da wakar solo din sa na farko da aka yi la'akari, wakar dijital "Promise", wanda ya shiga cikin wadanda suka rubuta ta, a cikin 2018 kuma ya yi rikodin duet "with you" tare da Ha Sung-woon sukai ma film na wasan kwaikwayo na TVN "Our Blues" a 2022. Jimin ya saki Album dinsa na farko na solo mai suna "Face" a cikin shekarar 2023. Ya y a Koriya ta Kudu da Japan, kuma na biyu a Amurka, yayin da wakarsa ta biyu mai suna "Like Crazy", ya yi karo na daya a kan Billboard Hot 100 na Amurka, inda ya yi. shi ne dan wasan solo na Koriya mafi girma a tarihi a kan Billboard 200 da Hot 100 a lokacin, kuma na farko da ya fara fitowa a saman teburin Billboard din. .[1]

Tasowarshi da karatunshi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Park Ji-min a ranar 13 ga Oktoba, 1995, a gundumar Geumjeong, Busan, Koriya ta Kudu.Shi dan kabilar Miling Park ne.Yan gidansu sun hada da mahaifiyarsa, mahaifinsa , da kanensa. Lokacin yana karami, ya halarci Makarantar Elementary ta Busan's Hodong da Yonsan Middle School.A makarantar sakandare, ya halarci "Just Dance Academy", inda ya koyi popping da brekin.Kafin ya zama mai horarwa, Jimin ya yi karatun raye-raye na zamani a makarantar sakandare ta Busan kuma ya kasance babban ɗalibi a sashen rawa na zamani.Wani malami ya ba da shawarar cewa ya shiga wani kamfani na nishaɗi, wanda ya kai shi ga Big Hit Entertainment.bayan yayi nasarar cin gasar shiga cikin wadanda zaa horar domin zama mawaqi, ya cigaba da karatunshi a shekarar 2012, ya koma makarantar sakandaren fasaha ta Koriya, ya kammala karatunsa a 2014.Jimin ya kammala karatunshi daga Jami'ar Cyber ​​​​Global a watan Agusta 2020 inda yayi digirinsa akan watsa labarai da bada nishadi, A shekarar 2021, yayi rijista a Jami'ar Hanyang Cyber, domin cigaba da samun masta digiri a fannin Gudanar da Kasuwanci a Talla a Kafofin watsa labarai. [2]

Daukakarsa[gyara sashe | gyara masomin]

Jimin shine cikon mai horarwa na karshe da aka kara zuwa jeri wanda a karshe zai zama dan qunguyar BTS. Daga cikin mambobi bakwai na kungiyar, ya shafe mafi kankanta lokacin—watanni shida—a matsayin mai horarwa kafin fara halarta. A ranar 13 ga Yuni, 2013, ya yi muhawara a matsayin mawaki kuma dan rawa a cikin BTS tare da wakar "No dream" daga farkon album dinsu na "2 Cool 4 Skool". A karkashin sunan kungiyar, ya fitar da wakokin solo guda uku: "Lie", "Serendipity", da "filter". An saki "Lie" a cikin 2016, a matsayin wani bangare na kundin studio album dinsu na Koriya na biyu, "Wings".[3]An kwatanta wakar a matsayin mai ban mamaki, yana isar da saƙo mai duhu da motsin rai daidai da ainihin ra'ayi na kundin [album] din. Sabanin, "Serendipity", daga kundinsu na" love yourself" a (2017 EP), wakar ta kasance mai laushi da sha'awa, tana bayyana farin ciki, yakini, da sha'awar soyayya. "filter", waƙa daga BTS' 2020 album studio Map of the Soul 7:, yana da fa'ida ta Latin, tare da waƙoƙin da ke nuna bangarori daban-daban na Jimin da yake nunawa duniya da na kusa da shi[4].

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 고, 대현 (May 22, 2021). "[움짤] 방탄소년단(BTS) 지민, 글로벌 버터 '꽃받침'~" [[Animated Pics] Bangtan Sonyeondan (BTS) Jimin, Global Butter 'Blooming Flower']. iMBC 연예 (in Korean). Archived from the original on January 23, 2024. Retrieved January 23, 2024.
  2. Dong, Sun-hwa (October 15, 2018). "Guess who? BTS members' pre-debut photos revealed [PHOTOS]". The Korea Times. Archived from the original on December 7, 2019. Retrieved October 18, 2018.
  3. Herman, Tamar (June 20, 2017). "Get to Know BTS: Jimin". Billboard. Archived from the original on May 2, 2020. Retrieved October 17, 2018.
  4. Dong, Sun-hwa (October 15, 2018). "Guess who? BTS members' pre-debut photos revealed [PHOTOS]". The Korea Times. Archived from the original on December 7, 2019. Retrieved October 18, 2018.