Kalma me harshen damo
Kalma me harshen Damo[gyara sashe | gyara masomin]
Kalma me harshen damo shine kalma me ma'ana fiyeda guda ɗaya.[gyara sashe | gyara masomin]
Misali: Gari, dama da sauran su.
GARI[gyara sashe | gyara masomin]
Gari yana nufin wajen zama ta mutane, muhalli inda kuma mutane fiye da biyu seke yin rayuwar su, maraya kenan Wanda akwai gida je da gonakai da sauran su.
- Azam ya tafi garin Hadeja.
- Ranar asabar itace kasuwar Danchuwa.
- Akwan tireloli dayawa agarin potiskum.
GARI[gyara sashe | gyara masomin]
GARI ita ce babbar riga ko bunjuma da ba haushe yake sakata ayayin biki, musamman ango, ko kuma wani babbar mutum medaraja acikin al'umma.
Wani lokacin ana kirantada malum-malum, amma  mafiyawa ana satane domin Kure adaka.
- Ango yayi dainkin gari dashi da abokan sa.
- Adamu baya son gari me aljuhu.
GARI[gyara sashe | gyara masomin]
GARI itace nikakken alkama, gero ko dayawa
Wanda ake amfani dashi wajen yin tuwa.
- Bana garin masara tayi tsada sosai.
- Injin gagale sun iya nika gari da laushi.
DAMA itama wanan kalmace me ma'ana fiyeda guda daya.[gyara sashe | gyara masomin]
DAMA[gyara sashe | gyara masomin]
Dama yana nufin samun sukuni, ko gamon katar.
misali:
- Oranga yace "idan yasamu dama zai zo ku gaisa".
- Salma taje har Kano amma bata samu damar ganin Ali Nuhu ba.
DAMA[gyara sashe | gyara masomin]
Itama wannan kalma ta dama tana nufin hada garin wani abu da ruwa, ko hada daskararren abu da wani narkakken abu.
Misali:
- Fatima ta iya dama Fura da nono.
- Aisha ta dama kunun Aduwa jiya.