Khalil Al-Qari

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Khalil Al-Qari
Rayuwa
Haihuwa Muzaffarabad, 1940
ƙasa Saudi Arebiya
Mutuwa Madinah, 3 Satumba 2018
Makwanci Al-Baqi'
Ƴan uwa
Yara
Karatu
Harsuna Larabci
Urdu
Ɗalibai
Sana'a
Sana'a Ulama'u da Malami
Employers Jami'ar Imam Muhammad ibn Saud Islamic  2018)

Khalil bin Abd al-Rahman al-Qari (Shekarar alif dubu ɗaya da ɗari uku da sittin da ɗaya bayan hijira 1361 AH / zuwa shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari tara da arba'in 1940 - ashirin da ukku 23 Dhu al-Hijjah shekarar alif dubu ɗaya da ɗari huɗu da talatin da tara bayan hijira 1439 AH / ukku 3 ga watan September, shekarar alif dubu biyu da goma sha takwas 2018), shi akewa laƙabi da Malamin limaman Masallatan Harami guda biyu, kuma ana ɗaukarsa ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa makarantar Modern Qur'anic Renaissance.[1][2]

An haifi Khalil Al-Qari a Muzaffarabad a shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari tara da arba'in 1940, kuma ya yi karatu a wurin Sheikh Muhammad Suleiman a Lahore, kuma a wajen mahaddaci Anwar Al-Haq. Ya haddace Alqur'ani mai girma daga Sheikh Fadl Karim, sannan ya karanta " Qira'at " akan " Qur'a " na Pakistan. A Pakistan ya yi aiki a matsayin mai gabatar da shirye-shiryen gidan rediyo a yankin Muzaffarabad.[3][4][5]

A shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da sittin da uku 1963 ya yi hijira zuwa Makkah Al-Mukarramah, ya yi karatu a masallacin Bin Laden da masallacin Harami. Ya karantar a Masallacin Harami, da Cibiyar Al-Arqam Bin Abi Al-Arqam da ke Al-Safa. Sannan kuma ya koma Madina, aka naɗa shi malami a cibiyar Ilimi ta Jami'ar Musulunci ta Imam Muhammad Ibn Sa'ud da ke Madina, inda ya zauna ya duƙufa wajen karantar da Alqur'ani mai girma.

Ana kiransa da " Malamin limaman Masallatan Harami biyu "; Dangane da cewa shida 6 daga cikin tsoffin ɗalibansa sun kasance limaman babban masallacin Makkah, tare da wasu fitattun ɗaliban da suka haɗa da Sheikh Muhammad Ayyub da Sheikh Ali Jaber.

Ana yi masa kallon jagaba a wajen karatun Al-qur'ani a makarantar Hijazi, kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa ƙungiyoyin bayar da agajin haddar Al-qur’ani a ƙasar Saudiyya. Shine mahaifin Muhammad da Mahmud limaman masallacin Annabi (S A W).

Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Ya rasu a ranar Litinin ashirin da uku 23 ga watan Zul-alHijjah shekarar alif dubu ɗaya da ɗari huɗu da talatin da tara 1439 Hijiriyya daidai da uku 3 ga watan Satumba, shekarar alif dubu biyu da goma sha takwas 2018, a Madina, yana da shekaru saba'in da takwas 78, kuma an binne shi da asuba a makabartar Al-Baqi.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "وفاة شيخ أئمة الحرمين خليل القارئ | إرم نيوز‬‎". web.archive.org. September 4, 2018. Archived from the original on 2018-09-04.
  2. "وفاة الشيخ "خليل القارئ" شيخ أئمة الحرمين الشريفين". web.archive.org. September 4, 2018. Archived from the original on 2018-09-04.
  3. "بوابة الفجر: وفاة شيخ أئمة الحرمين الشريفين". web.archive.org. December 4, 2018. Archived from the original on 2018-12-04.
  4. "خليل عبد الرحمن القارئ - طريق الإسلام". web.archive.org. September 4, 2018. Archived from the original on 2018-09-04.
  5. "بعد رحيله.. تعرف على سيرة شيخ أئمة الحرمين خليل القارئ". web.archive.org. September 4, 2018. Archived from the original on 2018-09-04.