Jump to content

Lamba (Tubani)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Asali da Tushe[gyara sashe | gyara masomin]

Lamba ko kuma Tubani kamar yadda aka san sunan a kasar Hausa, abincin gargajiya ne wanda ya yi dubbannin shekaru da samuwa kuma ya shahara a shiyyar Afirka ta Yamma musamman cikin yankunan arewacin Najeriya da Nijar da kuma Cadi. Inda aka fi yinsa shi ne yankin arewa maso gabashin Najeriya cikin jahohin da suka hada da Bauchi, Yobe, Borno da kuma Gombe wadanda sun kasance jahohin da aka fi samun al'ummar Karai-Karai a cikin su wadanda suka kasance al'ummar da ake dangantawa da zamowa mutanen farko da suka kai ga samuwar shi irin wannan nau'in abinci a bisa kasantuwarsa na zamowa fitaccen abincin su na gargajiya. Tubani wanda al'ummar Karai-Karai ke kira da Lamba a harshen su, ya shahara sosai a wurin al'ummar Karai-Karai da ma sauran kabilun da suke makotaka da su.

Kayan hadi[gyara sashe | gyara masomin]

Saboda farin jinin da abincin yake da shi wanda yayi sanadin watsuwar sa a tsakanin sauran ƙabilu, kayan hadin Lamba ko Tubani kamar yadda sunan yake da harshen Hausa na iya bambanta da kari ko kuma ragin wasu abubuwan kadan daga yadda al'ummar Karai-Karai din suke yinsa tun asali, hakazalika ko a yankunan jahohin da al'ummar suke da karfin tasiri akwai wadandan sauye-sauyen wanda samuwar su ke da alaka da sauyawar zamani. Misali, akwai wadanda suke yin shi a cikin ganyen dawa wacce ake kira da suna (sharam) yawanci a kasashen al'ummar Karai-Karai har wayau kuma a na yinsa ta hanyar ɗaurawa a leda. Haɗinsa duk kusan ɗaya ne bambanci kawai sai dai abinda ya zama ba dole sai an yi amfani dashi ba. Lamba a na yinsa ne da garin masara ko kuma garin dawa wasu su kan iya karawa da fulawa sannan ana saka wake da kuma karkashi da kanwa. kusan a na iya cewa duk tubanin da ya rasa daya cikin wadancan abubuwa to bai amsa sunan sa ba.

Yankunan da suka fi shahara wajen yi da sunan da suke kiransa[gyara sashe | gyara masomin]

  • Arewa maso gabas; Yobe, Bauchi, Borno, Gombe (Lamba)
  • Arewa maso yamma; Kaduna, Kano, Katsina, Sokoto, JIgawa (Lamba/Tubani), Kebbi, Zamfara (Tubani)
  • Jamhuriyar Nijar (Tubani)

Amfanin shi[gyara sashe | gyara masomin]

Da shi ke yana tattare da kayan hadi iri daban-daban kusan kowanne yana da amfani na musamman ga lafiyar dan adam kamar filawa yana kara hasken ido dayake yana tattare da sinadarin bitamin A, sannan wake furotin ne shikuma masara da dawa carbohydrate ne.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

[1] [2]

  1. https://cookpad.com/ng/recipes/6474822-lamba
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-01-18. Retrieved 2022-01-17.