Muhammed Idris Malagi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Muhammed Idris Malagi
Rayuwa
Sana'a

Mohammed Idris Malagi wanda aka fi sani da Malagi (an haife shi a ranar 2 ga watan Mayu shekarar 1966) marubucin Najeriya ne, kwararre kan hulɗa da jama'a, kuma ɗan siyasa wanda shi ne ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a a Najeriya. Shugaba Bola Tinubu ne ya naɗa shi a watan Agustan 2023. Shine shugaban kuma wanda ya ƙirkiri gidan jaridar Blueprint newspaper. Shi ne kuma shugaban kamfanin Kings Broadcasting Limited na Abuja, masu gidan rediyon WE 106.5 FM Abuja, Nigeria. Ya kuma kasance babban sakataren ƙungiyar masu masu gidan jaridu ta Najeriya . Ya kasance daraktan yaɗa labarai na kwamitin yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC Tinubu-Shettima.[1][2]

Rayuwar farko da Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Mohammed Idris a ranar 2 ga watan Mayu shekarar 1966 a karamar hukumar Gbako ta jihar Neja. Ya yi karatun firamare a Kontagora tsakanin shekarar 1971 zuwa 1977. Daga nan sai ya wuce GSS Rijau a shekarar 1977 inda ya kamala a 1982. A shekarar 1983 ya samu gurbin karatun harshen Turanci a Jami’ar Usmanu Danfodiyo, inda ya kammala a shekarar 1987. Ya yi karatun digirinsa na biyu a wannan fanni a Jami’ar Bayero Kano a shekarar 1995.

Aiki/Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

A watan Mayun shekarar 2011, Idris Malagi ya kafa jaridar Blueprint kuma shine yake shugabantar ta tun lokacin. Shi ne kuma wanda ya kafa kuma shugaban ƙungiyar Bifocal.A watan Disamba shekarar 2020, an zaɓe shi babban sakataren ƙungiyar masu mallakar jaridu ta Najeriya. A ranar 27 ga watan Nuwamba, shekarar 2019, ya karɓi ikon mallakar gidan rediyon Kings Broadcasting Network, masu kamfanin WE 106.5 FM Abuja.

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Mohammed Idris Malagi, a matsayin ɗan jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya kasance ɗan takarar gwamna a jihar Neja a babban zaɓen Najeriya na 2023. Ya samu ƙuri'u 154 sannan kuma ɗan majalisar wakilai Umar Bago ya samu kuri'u 386. An naɗa shi daraktan sadarwa na dabarun sadarwa na Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Presidential Campaign Council (PCC).[3]

Taimako da Jinƙai[gyara sashe | gyara masomin]

Idris Malagi shine wanda ya kafa gidauniyar Mohammed Idris Malagi.

Kyaututtuka da kKarramawa[gyara sashe | gyara masomin]

Alhaji Mohammed Idris Malagi yana riƙe da sarautar gargajiya ta Kakaaki Nupe, sarautar da Yahaya Abubakar, Etsu Nupe ya ba shi. Taken ya kasance don karramawa da taimakonsa ga jama'a da nasarorin da ya samu a fagen yaɗa labarai da hulɗa da jama'a. A ranar 8 ga Disamba, 2022, ƙungiyar 'yan jarida ta Najeriya ta ba shi lambar yabo ta Milestone Recognition Media Icons in Nigeria.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Lawal, Ahmid (9 December 2020). "Blueprint publisher now NPAN scribe as Trust chair leads new team". Blueprint Newspaper. Retrieved 12 July 2023.
  2. Daily Trust Online (8 December 2020). "Daily Trust's Kabir Yusuf Named President Of Newspaper Owners". Daily Trust. Retrieved 12 July 2023.
  3. "PDF" (PDF). The Cable. Retrieved 27 August 2023.