Oluchi Onweagba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Oluchi Onweagba
Rayuwa
Haihuwa Lagos, 1 ga Augusta, 1982 (41 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Ƴan uwa
Yara
Karatu
Makaranta New York University (en) Fassara
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a model (en) Fassara
Tsayi 183 cm
IMDb nm1493799
oluchi.com

Oluchi Onweagba-Orlandi (an haife ta a ranar 1 ga watan Agustan shekarar 1980) 'yar Najeriya ce dake zaune a Birnin New York. Lokacin da ta girma a unguwannin bayan gari na Legas, ta ci gasar kyau ta "The Face of Africa" tun tana 'yar shekara 16.

Onweagba ta girma ne a cikin unguwannin bayan gari na Legas a Nijeriya, tare da kuma 'yan uwanta maza guda biyu da kuma mata. Ita diya ce ga ma'aikacin gwamnati mahaifiyar ta kuwa ma'aikaciyar jinya ce.

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan ta koma New York City, inda take zaune har yanzu, ta fara bayyana ne a cikin shafukan mujallan Amurka da Italia Vogue, Harper's Bazaar, Marie Claire, Allure, Nylon da W.[ana buƙatar hujja] Oluchi ta fito a bangon mujallar Italia mai sunaVogue, Elle, iD, Pop, Untold, da kuma Surface.

Ta yi aiki da mutane irinsu Gucci, Carolina Herrera, John Galliano, Missoni, Tommy Hilfiger, Chanel, Bottega Veneta, Christian Dior, Alessandro Dell'Acqua, Jeremy Scott, Helmut Lang, Fendi, Anna Sui, Givenchy, Kenzo, Giorgio Armani, Céline, Nina Ricci, da Diane Von Furstenberg .

Iyali[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 2006, Onweagba ta auri wani mai tsara ado ɗan kasar Italiya Luca Orlandi. Sun kasance abokai na dogon lokaci sosai kafin suyi aure. Suna da yara maza biyu kuma suna zaune a New York. Ɗan su Ugo Ugochukwu - ya kasance mai ƙwazo a tseren Kart .

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]