Shirley Cloete (an haife ta a ranar 2 ga watan Agustan shekara ta 1986) ƴar wasan ƙwallon ƙafa ce ta Namibia wacce ke taka leda a matsayin ƴar wasan tsakiya a tawagar mata ta Namibia . Ta kasance daga cikin tawagar a Gasar Cin Kofin Mata ta Afirka ta 2014. A matakin kulob ɗin ta buga wa Okahandja Beauties FC a Namibia.[1][2]