User:Ubaiduyau

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

TALAKA SAI HAKURI... Ana yi wa Najeriya  kirari  da uwa mai ba da mama ga dukkan kasashen da ke nahiyar Afirka, kamar yadda Jihar Kano ta yi fice ana yi mata kirari da jalla babbar Hausa, mai mata, mai mota, mai  Dala da Gwauron Dutse ko da me ka zo an fi ka. To a saninmu Najeriya ta yi kaurin suna matuka gaya ,amma ba a nan gizo ke sakar ba, a yau na fahimci tana kasa tana dabo, tana tare da tarin matsaloli iri-iri da suka gallabi ’ya’yanta karancin makamashin hasken wutar lantarki; barazana ga sha’anin ci gaban ilimi; rashin ingantaccen tsaro a kasa; durkushewar kiwon lafiya; rashin aikin yi  ga matasa; rashin gudanar da zaben yadda ya kamata;  faduwar darajar aikin noma. karancin makamashin wutar lantarki a yau a Najeriya kwalliya ta kasa biyan kudin ruwa ballantana na sabulu. Duk da cewa wutar lantarki ita ce linzamin farko na ayyuka da kowane dan Najeriya yake riko da shi, an dogara da komai a kan wutar lantarki. Rashin ta ya haddasa mummunar faduwar  tattalin arzikin ’yan Najeriya, musamman masana’ antu da bangarori iri-iri. Hakan ya yi sanadiyyar tashin  farashin kayan  masarufi a Najeriya, da kuma bude hanya ta shigo da kayayyakin da masana’antun waje suka sarrafa, baje hajarsu a Najeriya da cin karensu babu babbaka, ya kuma sanya kayan da ake sana’antawa  su ki sayuwa. Talakawa sun fada tsaka mai wuya ita ma gwamnati hankalinta ya kasa kwantawa, to wannan da me ya yi kama? Alhali megawat da ake da shi na yunkurin karfin hasken wutar lantarki da muke da shi a da yana da matukar wadatar da Najeriya ciki har tsakura wa jamhuriyar Nijar muke yi. Mutuwar masana’antu ya kara yawan alkaluman marasa aikin yi a Najeriya  ya kara yawa. Haka yasa ala tilas masana’ antu dari da sittin da daya( 161) suka tattara komatsansu ala tilas zuwa kasar Ghana da tauraruwarta take ci gaba da haskawa ta fannoni iri-iri. Wannan ya faru karara muna gani gwamanti ta kasa shawo kan lamarin. A bin takaici ba ya karewa a Najeriya, shugaban kasa Alhaji Umaru Musa ’Yar `aduwa ya yi alwashin yin bincike na ba  -sani –ba- sabo game da ba da kwangilolin wutar lantarki da aka yi rub- da- ciki aka yi. Talakawa da masu kishin kasa sun yi matukar maraba da labarin, amma har yanzu babu amo babu labarin sakamakon kwamitin bincike balle a yi tunanin gurfanar da masu laifi marasa kishin kasa  a gaban kuliya manta sabo. Wannan sai a Najeriya! Shin a haka za mu ci gaba da tafiya da kuma tunkaho da uwa ba da mama ga kasashen Afrika? Abin kunya, wai rakumi ya shanye ruwan kaji. An ce idan kura na maganin zawo ta yi wa kanta. Ya kasance mu talakawan Najeriya akwai hakuri, amma fa ba ma bukatar kura ta kai mu bango.  A wata hira kamar almara da aka yi da ambasada Ibrahim Kazaure a gidan rediyon BBC ya shaida wa ’yan Najeriya cewa ’Yar `aduwa yana wani shiri wai abin burgewa na gyaran hasken wutar lantarki  zuwa watan Disamba na shekarar  dubu biyu da tara( 2009) to ansha ruwa kasa tana tsotsewa, rana ba ta karya, a yadda ’yan Najeriya rayuwa ta yi musu daurin mintin tom-tom akwai wata maganar da za ta sanyaya zuciyarsu kuwa a wannan lokaci idan ba su gani a kasa ba. Gashi dai shekarar 2010 ta shigo sai kaka? 2. Barazana ga tabarbarewar sha’anin ilimi, abin yana ci mana tuwo a kwarya ganin yadda a kasafin kudin kasa na kowace shekara ake ware makudan kudade wajen gudanar da harka ilimi, amma talakawa ba sa gani a kasa. A kullum tambayar su a ina kudaden suke makalewa ba tare da sun kai ga inda aka ce ba? To ku sani an yi walkiya mun gane makiyanmu na hakika da ba sa bukatar ’yan Najeriya talakawa su samu ilimi nagari. Duk da cewa ba a kyauta ake nemansa ba, su kuwa mun sani Turawa ne suka dauki nauyin su gaba daya,amma abin mamaki mu fara duba fannin mataki na farko watau firamare, babu kayan aiki, babu albashi mai tsoka ga su kan su malaman da suke koyarwa an maishe su dabbar kiwo. Abin bakin ciki baya karewa shekarun baya da suka gabata aka fito da wani sabon tsari na baiwa karatun a firamare na bai daya kyauta, duk da sanin asusun majalisar dinkin duniya na ba da makudan kudade wajen ganin an cimma ilmantar da yara, haka ita ma Hukumar da ke son ganin cimma muradun  karni watau MDG  tana iya kokarinta wajen ganin an samu nasara. Ba su sani cewa malamai sai a shafe watanni  biyar ba a biya su alawus na dubu goma kacal ya gagari gwamnati; To da haka ake neman cimma burin? Wannan ba zai yiwu ba, sai an yi gyara sosai.  Haka ita ma sakandare, sai ka tarar babu kayan aiki babu kujeru, matsalar dai kusan guda ce illa dan bambance -bambance da ake samu. Ita kuwa jami’a har yanzu ba ta farfado daga nakasar yajin aiki da ta dawo na watanni kusan biyar, bisa bukatu na malaman jami’o’i da suka zayyana wa gwamnati sai ta biya su bukatun su koma aikin. Shi ma akwai rashin albashi mai tsoka; rashin dakunan karatu, da rashin kayan aiki, da sauran abubuwa da suke ci musu tuwo a kwarya.’ Yan kasa sun fiyawan zargin cewa babu ’ya’ yansu a cikin makarantun sun kaisu kasar waje domin su yi karatu, babu yadda za su yi su damu da makarantun cikin gida ko suna gudana daidai, hakika batun ya sanya tashin jijiyar wuya da tabka muhawara a kafofin yada labarai da jaridun ciki da wajen kasarnan na ganin ilimi ya wadata  da kuma yin gyara a fannin ilimi.  mai karatu abin da na ambata na ciwa ’yan Najeriya tuwo a kwarya matuka. Sai dai rokonmu gwamnati ta yi gyara don ci gaban kasarta. 3. Rashin ingantaccen tsaro. Burin kowace gwamnati ce ta fara sa harkar tsaro a sahu na farko-farko domin bankwana da fargaba da kwararowar abokan gaba, ko da kuwa ta soja ce ko farar fula. Ita dai gwamnati ba ta son a fito fili a ce babu cikekken tsaro a kasa duk da cewa mun sani tana iya kokarinta , amma an ce dambu idan ya yi yawa ba ya jin mai. To mu dubi yadda, ba dare babu rana,  ’yan fashi da makami a cikin kasar nan suke sanadiyyar kisan rayukan talaka da masu kudi; yawaitar ’ yan damfara a fili. Ga kuma yawan cafke makamai kamar wanda aka kama a filin jirgin Malam Aminu Kano, jirgi na makare da kayan yaki. Sannan a baya –bayan nan jami’an shige da fice na kwastan a bakin ruwa sun samu nasarar cafke wata kwantena makare da makamai. Abin tambaya shi ne sai a ce za a yi bincike amma sai ka ji shiru da haka zancen yake susucewa. Haka tasa ake cewa tsaro a Najeiya da sauran aiki, su ma gwamnatin ba’a bar su  ba domin sai a wannan lokacine a ka taba samun masu garkuwa  har sai anbiya musu bukatunsu. Ciki ya hada da cafke jami’ar kasar waje, na baya- bayan nan har da sakataren  gwamnatin Jihar Kaduna. To shin ko wane irin mataki gwamnati za ta dauka, domin ’yan kasa sun fusata da wannan lamari na ganin cewa dole gwamnati ita ce da nauyin magance matsasar duk da cewa hakika ga mai karanta jaridu da sauraron gidajen radiyo da talabijin yana gani ko jin yadda jami’an tsaro suke cafke masu laifi sai dai hukunta su shi ne matsalar.