Usman Bala Zango

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Usman Bala Zango (an haifeshi a ranar 3 ga Janairun, 1963). Kani ne ga Alh. Sani Zangon-Daura. Rt. Hon Usman Bala, ɗan kasuwa ne kuma gogaggen ɗan-siyasa. Shine Kakakin Majalisa na farko a Jihar Katsina.[ana buƙatar hujja] Ya riƙe mukamai daban-daban a kamfanoni mabanbanta. Shine shugaban daya kwamitin amintattu na Maryam Endowment Fund.

Farkon Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Ya fara karatun sa na firamare a Zango One Primary School daga shekarar 1972 zuwa 1978. Daga nan ya zarce Government Secondary School Bauci daga shekarar 1978 zuwa 1981. Ya anshi kwalin WASCE a Government Secondary Funtua 1981 zuwa 1983. Ya kuma halarci Kaduna Polytechnic daga shekarar 1983 zuwa 1986 in da ya anshi shedar kamala National Diploma a fagen Business Administration.

Mukami da aiki[gyara sashe | gyara masomin]

  • Ya rike Mukamin accounter a Hukumar Lafiya ta Jihar Katsina 1988 zuwa 1991.
  • Shine Kakakin Majalisa na farko na Jihar Katsina daga 22 ga Janairu, 1992 zuwa 17 ga Nuwamba, 1993.
  • Commercial Manager Nation House Press Fabarairu, 1994 zuwa Disamba, 1995.
  • Adminin and Personal Manager Kaduna Aluminium Extrusion Ltd Oktoba, 1998 zuwa Oktoba 2002.
  • Kaduna Machine Works and Kaduna Aluminium Oktoba, 1998 zuwa Oktoba 2002.
  • Maibada Shawara na Musamman akan Harkokin Siyaya ga Gwamnan Jihar Katsina  Mai-Girma Aminu Bello Masari Ogusta, 2015 zuwa 29 ga Mayu, 2019.
  • Shugaban Gudanarwa Maikano Digital Printing and General Services Ltd. 17 ga Yuni, 2019 har zuwa yau.
  • Shugaban Board of Trustee na Maryam Endowment Fund, 2012 zuwa yau.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]