Ƙwayar Hatsi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Hatsi kwaya ce dake fitowa daga cikin karkashin ƙasa ta hanyar shukata da manomi keyi harta kai matakin da za'a girbe ta. Hatsi ƙwayar halitta ce da duk wani dan'adam dake doron ƙasa sai yayi amfani da ita wurin gudanar da Rayuwar shi ta yau da kullum. shi dai wannan ƙwayar Hasti yakan yi nunar sa ne ayayin da aka fuskanta ce kaka tayi wato lokacin iska,bayan an shafe watanni shida ana ruwa sama kamar da bakin kwarya harta kai da wannan shukar tayi girma ta fitar da amfanin agare ta.a irin wannan lokaci manoma sukanyi murna shiga irin wannan lokaci harta kai da sunyi tanajin abin auren ƴaƴansu.

Ire-iren ƙwayar Hatsi[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai;

  1. Gero
  2. shinkafa
  3. masara
  4. Dawa
  5. Maiwa
  6. Alkama
  7. wake. Dadai sauran su.

Gero[gyara sashe | gyara masomin]

Gero ƙwayar hatsi ne da yake fitowa a karkashin ƙasa a yayin da Damina ta sauka,a daidai lokacin da manomi ya gane cewa Damina ta kama yakan ziyarci Gonar sa domin yayi shara,ya kuma yi aikace-aikacen sa kafin ya zuba taki ya fara Noma.

Shinkafa[gyara sashe | gyara masomin]

shinkafa ƙwayar Hatsi ne da take fitowa a karkashin ƙasa Musamman wuri da yake da danshi,akanyi Noman shinkafa a cikin damina,bayan rani manomi yakan girbi ta.

Masara[gyara sashe | gyara masomin]

ƙwayar masara, ƙwaya ce data ke fitowa a doron kasa bayan manomi yayi mata hidima har ta kai lokacin gibi,Masara tana da amfanin a jikin mutum dama sauran halittun kamar dabbobin Gida irin su kaji da dai sauransu.

Dawa[gyara sashe | gyara masomin]

Dawa ƙwaya ce dake fitowa daga karkashin kasa bayan anyi hidima nomata,tana da matuƙar amfani ajikin ɗan Adam musamman idan ya lazimta cin towon ta ko kunun ta,akanyi giya da ita musamman kanfanoni.

Maiwa[gyara sashe | gyara masomin]

ƙwayar Hatsi ta maiwa kamar gero take ammah kowacce akwai Amfanin ta a jikin ɗan Adam, mutanen karkara su kanyi kokon maiwa.

Alkama[gyara sashe | gyara masomin]

ƙwayar Hatsi na Alkama ƙwaya ce dake fita daga cikin ƙasa,kuma dai ita Alkama tafi son wurin sanyi.manoman ta sukan shukata kafin ruwa ya dauke.al'umma sukanyi amfani da alkama wurin yin [ [girke-girke]] sannan akwai sina darai masu matuƙar amfani a jikin mutum.

Wake[gyara sashe | gyara masomin]

wake ƙwayar Hatsi ne da yake da matukar tasiri a jikin mutum, manoma suna da himma wurin shuka wake a irin yankunan arewacin Najeriya kamar jahohin arewa maso yamma da arewa maso gabas.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]