Arsenal

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Arsenal

Arsenal Football Club (anfi sanin team din da suna Arsenal) ƙungiyar kwararrun yan kwallo ce ta ingila. Wadda take a Holloway da kuma north London. Arsenal tana ɗaya daga cikin ƙungiyoyi masu fafatawa domin lashe gasar. Arsenal ta samu nasarar lashe gasar hau sau goma sha ukku 13. Sannan da cikin goma sha ukku 13 dinnan tayi nasar lashe gasar ba tare da wata ƙungiyar ta doke ta ba koda sau ɗaya1. Sannan ƙungiyar Arsenal ɗin ta samu nasarar lashe gasar F. A cup har guda goma sha huɗu14. Sannan ƙungiyar ta samu nasarar cin league cup har guda biyu 2. Sannan ta samu nasarar lashe gasar community shield guda goma sha bakwai 17. Da kuma Football League Centenary Trophy. Saidai a gasar nahiyar turai, sunci kofi ɗaya 1 tilo wanda ake kira da suna European Cup Winners' cup da kuma wani kofi da ake kira inter cities fairs cup. Akuma ɓangaren nasarar lashe kofuffuka, ƙungiyar itace a gurbi na ukku 3 a ɓangaren ƙungiyoyin Ingila.

Arsenal itace ƙungiya ta farko da ta fara buga gasar League a kaf kudancin ingila a shekarar alif dubu ɗaya da ɗari takwas da casa'in da ukku 1893. Sannan ta fara buga babban League din na ƙololuwa a shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da huɗu 1904. Sannan ƙungiyar ta buga League din gajiyayyu sau ɗaya kacal a shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da goma sha uku 1913, daga nan kuma sai ƙungiyar ta cigaba da gwagwarmaya da fafutuka a cikin gassr League ɗin. Sannan ta kasance ƙungiya ta biyu wajan yawan buga wasanni a cikin gasar. A shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da talatin 1930, Arsenal tayi nasarar lashe League Championships guda biyar 5 da kuma FA Cups guda biyu 2, da kuma wani FA Cup da kuma Championships guda biyu 2 bayan yaƙin. A shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari tara da saba'in zuwa shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari tara da saba'in da ɗaya 1970 - 71, taci babban League da kuma FA cup har sau biyu 2. Daga shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da tamanin da biyar 1985 da shekara ta alif dubu biyu da biyar 2005, ƙungiyar ta samu nasarar lashe gasar League din har sau 5 da kuma FA cup da kuma wasu ƙarin biyu. Ƙungiyar ta kammala ƙarni na ashirin 20 da mafi average na ƙarewa daga teburin League ɗin. A tsakanin shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa'in da takwas 1998 da shekara ta alif dubu biyu da goma sha bakwai 2017, Arsenal ta samu nasarar tsallakwa zuwa buga gasar zakarun Turai har sau goma sha tara 19 a jere amma sedai abun ya ƙare ne bayan buga wasanni talatin da takwas 38 a shekarar alif dubu biyu da goma sha bakwai 2017 lokacin da ƙungiyar ta gama a mataki na biyar a teburi, maki ɗaya ne kawai ya rabata da wanda ke na huɗu, wannan ƙungiya itace Liverpool.

A shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari takwas da tamanin da shida 1886, ma aikan haƙo makamai a royal Arsenal a Woolwich sun gano ƙungiyar a dial square. A shekarar alif dubu ɗaya da ɗari da goma sha ukku 1913 ƙungiyar ta tsallako gari zuwa filin wasa na Arsenal a Highbury, sannan suka zamo maƙota da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham Hotspur, sannan hakan yasa aka ƙirƙiri north London derby saboda hamayya dake tsakanin ƙungiyoyin guda biyu. Herbart Chapman yacima ƙungiyar kyautar silver tun farko, sannan kwar jininsa ne ya kawo nasarori wajan lashe kofi a shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da talatin 1930 ya taimaka wajan bayyanar da WM formation, floodlights, da kuma shirt numbers; sannan kuma ya ƙara fari ya kuma haska ja a jikin rigar ta ƙungiyar Arsenal.

Arsene Wenger ya kasance mai bayar da horo mafi daɗewa a tarihin wannan ƙungiyar, sannan yafi Kowane mai bada horo nasarar lashe kofuffuka a tarihin ƙungiyar. Ya samu nasarar lashe FA cup guda bakwai, sannan shine mutum ɗaya tilo a gasar da ya shafe wasanni arba'in da tara 49 ba tare da wani ya doke shi ba. Ya samu wannan nasara na a 2003 -2004 inda mutane suka sa musu suna da Invisibles Ma'ana "Wadanda basu dokuwa".

a 2006 ƙungiyar ta matsa cikin emirates stadium inda suka kashe kuɗi kimanin £366.1m a 2021-2022. An ƙididdiga kuɗin ƙungiyar inda suka kai kimanin Us bilitan biyu da digo shida 2.6 billion by Forbes, inda suka kasance a mataki na goma a duniya cikin waɗanda sukafi kowa kuɗi duniya sannan kuma ƙungiyar tana ɗaya daga cikin ƙungiyoyi waɗanda akafi bibiya a cikin kafar sada zumunta. Taken ƙungiyar shine "Victoria Concordia Crescit, Latin for "Victory Through Harmony.".

TARIHI

Tarihin Arsenal (1886 - 1966), tarihin Arsenal daga (1966 zuwa yanzu) da kuma ma'ajiyar tarihin Arsenal


1886–1912: daga Dial Square zuwa Arsenal

A October, 1886 Scotsman David Danskin da ma'aikatan haƙo makamai guda goma sha biyar 15 a Woolwich sun haɗa dial square ta ƙungiyar ƙwallon ƙafa, aka samata suna bayan taron workshop a zucitar royal Arsenal complex. Kowane mamba ya bada gudunmawa sosai sa danskin shima ya ƙara shilling guda ukku saboda a taimaka ma ƙungiyar. Dial square sun buga wasan su a 11 ga watan Disamba, 1886 suda eastern wanderers, sannan sun samu nasarar lallasa su da ci 6 - 0. An sama ƙungiyar suna royal Arsenal Watanyyy. Sannan gidanta na farko shine Plumstead Common duk da cewa sun kwashe tsawon lokaci suna wasa a manor wuri, kofunansu na farko shine Kent Senior Cup da kuma London Charity Cup a 1889-1890 da London Senior Cup a 1890-91. Waɗannan sune kofunan da Arsenal ta lashe lokacin da take a kudancin landan. A 1891, Royal Arsenal ta zama ƙungiya ta farko da ta fara buga gasa ta masu mafi ƙwarewa a harkar ƙwallon ƙafa. An sake canzama Royal Arsenal suna a karo na biyu lokacin da ta zama kamfani mai zaman kanta a 1893





Manazarta

https://en.wikipedia.org/wiki/Arsenal_F.C.[gyara sashe | gyara masomin]