Kathmandu (lafazi : /katmandu/) birni ne, da ke a ƙasar Nepal. Shi ne babban birnin ƙasar Nepal. Kathmandu yana da yawan jama'a miliyan biyu da dubu dari biyar, bisa ga jimillar 2019. An gina birnin Kathmandu a karni na takwas kafin haihuwar Annabi Issa.