Anti-Fulani sentiment

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Anti-Fulani sentiment
sentiment (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na Wariyar launin fata da ideology (en) Fassara

Wariyar da ake nuna wa Fulani a Najeriya shi ne kiyayyar Fulani da ake yi musu a sakamakon haka. Fulani ƙabilar ce ta ƙabilar makiyaya da ta tarwatse a ƙasashen yammacin Afirka da dama. Fulani suna wakiltar kashi 6% na al'ummar Najeriya. [1]

Ƴan ta'addan dake jingina kansu da Musulunci[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin kowacce ƙabila akwai mutanen kirki akwai na banza a saboda haka ne ake zargin wasu daga cikin Fulani waɗanda ɓata gari, ne da suke tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci irinsu Boko Haram duk da cewa su kansu galibi suna fuskantar hare-haren ta’addanci. Waɗannan tuhume- tuhumen dai sun ƙara ƙarfafa ƙungiyoyin ‘yan ƙabilanci daban-daban a Najeriya, irinsu ƙungiyar ta'adanci ta IPOB waɗanda sun fito ne daga ƙabilar Igbo ta Indigenous People of Biafra wannan ƙungiya ta IPOB an kafa ta ne saboda ta'adanci ba wai kamar yadda ake ikirarin samun ƙasar ne ba, a dalilin haka kuwa ko su shugabannin yankin su basu yarda da IPOB ba. Haka ana yin amfani da wannan ƙungiya don yunƙurin yaɗa kalaman ƙyama ga Fulani da sauran duk wani yare da ya fito daga arewacin Najeriya.[2][3]

Rikicin makiyaya da manoma[gyara sashe | gyara masomin]

Rikicin makiyaya da manoma a Najeriya jerin rikice-rikice ne tsakanin Fulani makiyaya da manoma wadanda ba Fulani ba a kan filaye, wanda wani lokaci yakan haifar da tashin hankali. Gasar da ake yi da Fulani makiyaya ta ƙara zafafa kyamar Fulani a Najeriya daga ‘yan siyasa da kafafen yaɗa labarai. Dangane da wannan rikici, wasu jihohi a Najeriya sun ba da shawara ko kafa doka don hana Fulani makiyaya kawo shanunsu kiwo. Ana zargin wadannan dokokin da nuna wariya ga Fulani ba tare da magance matsalar ba. Kungiyar kare hakkin Fulani ta Tabital Pulaaku International ta zargi Sanatan Adamawa, Binos Dauda Yaroe da kalaman nuna kiyayya, bayan da ya zargi Fulani makiyaya da yin garkuwa da mutane a Najeriya.[4][5]

Lynchings[gyara sashe | gyara masomin]

Rikicin makiyaya da manoma ya haifar da kashe-kashen ƙabilanci ga Fulani. A ranar 1 ga Fabrairu, na shekara ta 2018, wasu Fulani 7 a Gboko, Jihar Benue, Najeriya, da ba a zarge su da aikata wani laifi ba, an kashe su a hannun wasu fusatattun mutane bayan sun yi garkuwa da su daga wata motar safarar jama’a. Bayan hare-haren da aka kai a kauyukan manoma na Berom a jihar Filato daga ranakun 23-24 ga watan Yunin 2018, matasan kabilar Berom a jihar Filato sun tare manyan hanyoyi suka kashe Fulani tare da lalata duniyoyin Fulani wanda ba'a san yawan dukiyar da suka ɓarnatar ba, a taƙaice ba'a san adadinsu ba . [6] Wasu fusatattun mutane a jihar Edo sun kashe wasu da ake zargin Fulani makiyaya ne su biyar da ke ɗauke da bindigogi.[6][6][7]

Gidan rediyon Fulani[gyara sashe | gyara masomin]

Shugabanin jihohin kudancin Najeriya da Middle Belt, sun bayyana rashin amincewarsu da shirin gwamnatin tarayya na kafa gidan rediyon da yaren Fulani, suna masu cewa za su yada farfagandar kisan kiyashi ga wadanda ba Fulani ba, inda suka kwatanta da kisan kiyashin da aka yi a kasar Rwanda.[8] Duk da cewa tabbas buɗe gidan rediyon zai ƙara fahimta tsakanin Fulani da sauran yaruku a duk faɗin Najeriya.

Kan layi[gyara sashe | gyara masomin]

A shekara ta 2016, a matsayin martani ga karuwar rigingimu da Fulani makiyaya, maudu’in #fulaniherdmen ya yi kamari a tsakanin masu amfani da shafukan sada zumunta na Najeriya, tare da zafafan kalaman ƙyamar Fulani ko da kuwa Fulanin ba basu da lsifi. Kafofin yada labarai na yanar gizo da labaran karya sun bayyana Fulani makiyaya a matsayin masu kisa ko ’yan ta’adda masu kisa, lamarin da ke kara zaburar da kyamar Fulani. Bishop din Katolika na Najeriya Matthew Hassan Kukah ya yi kira da a kawo karshen kalaman nuna kiyayya a yanar gizo ga Fulani makiyaya.[9][10][11]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Nigeria country profile at CIA's The World Factbook: "Fulani 6%" out of a population of 219 million (2021 estimate).
  2. Jessica Caus. Case 2: Nigeria (PDF) (Report). United Nations University.
  3. "Nigeria's Diverse Security Threats".
  4. "Nigeria's Anti-Grazing Laws Fail to Address the Root Causes of Rural Conflict". World Politics Review. March 16, 2018.
  5. Onimisi Alao, Yola (March 1, 2021). "Group fumes as tension over Sen Yaroe's 'anti-Fulani' comment persists". The Nation.
  6. 6.0 6.1 6.2 "Stopping Nigeria's Spiralling Farmer-Herder Violence". Crisis Group. July 26, 2018.
  7. "Disturbing video: Angry mob lynches Fulani herdsmen caught with firearms in Edo [Graphic] – TheNewsGuru".
  8. "Southern And Middle Belt Leaders Reject Fulani Radio Station Funded By Federal Govt". Sahara Reporters. May 23, 2019.
  9. Onimisi Alao, Yola (5 May 2016). "Making sense of Nigeria's Fulani-farmer conflict". BBC.
  10. "Fake news and Nigeria's herder crisis". BBC. 29 June 2018.
  11. "Nigeria: Bishop calls for end to hate speech against Fulani herdsmen". Independent Catholic News. 1 August 2019.