Farfesa Abdalla Uba Adamu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Farfesa Abdallah Uba Adamu, wanda ake ma kirari da Gangaran ka fi gwani!. (an haife shi ranar 25 ga watan Afir din shekarar 1956). Gogaggen masanin harkar ilimi; bajimin marubuci; fitaccen mai karantarwa a matakin ƙasa-da-ƙasa International Visiting Lecturer, ayyukan da yake da gogayyar shekaru arbai’in cif a cikin shekarar (1979 – 2019). Dambu mai hawa biyu, shi ne farfesa biyu a ɗaya, abin nuif, farfesa a fannonin ilimi guda biyu; Fannin Ilimin Kimiyya (Science Education) da kuma fannin Sadarwar Al’adu da Kafafen Sadarwa (Media and Cultural Communication) daga Jami’ar Bayero ta Kano.[1]

Allah yayi masa baiwa da fasahar magana, gogewa, jajircewa da kuma himma a fannonin da ya yi fice a kai, wato karantarwa, rubuce-rubuce da kuma gabatar da jawabai. Mutum ne shi mai son bai wa jama’a gudunmawa a fannin ilimi tare kuma da ƙarfafar guiwar na ƙasa da shi domin su taso. Gudunmawar da ya bayar wajen kawo sauyi a fagen yadda ake rubuta littattafan Hausa, abu ne mai wahalar taskacewa. Abdallah Uba Adamu, cikakken Bahaushen Kano ne da ke Jamhuriyar Tarayyar Najeriya.[2]

Haihuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An Kuma hafi Farfesa Abdallah Uba Adamu a ranar 25 ga watan Afirilun shekarar 1956, a cikin Unguwar Daneji da ke cikin ƙwaryar birnin Kano. Ɗane shi ga fitaccen marubucin tarihin Kano, wato Dakta Uba Adamu; marubucin littafin tarihin Kano mai suna Kano Ƙwaryar Ƙirar Matattarar Alherai, mujalladi na ɗaya zuwa na huɗu.[3]

Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1979: Digirin Farko a Fannin Ilimi, Kimiyyar Halittu da kuma Fishiyolojin(Education/Biology/Physiology), daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.[3]
  2. 1982: Difilomar Mai Zurfi (Postgraduate Diploma) a FanninnIlimin Kimiyya (Science Education), daga Kwalejin Chelsea ta Jami’ar London.
  3. 1983: Digiri na biyu a fannin Ilimin Kimiyya (Science Education), daga Kwalejin Chelsea ta Jami’ar London.
  4. 1988: Digirin Digirgir daga Jami’ar Sussex da ke Falmer, Brighton, England.
  5. 1997: Farfesa a Fannin Ilimin Kimiyya (Science Education), Jami’ar Bayero, Kano.
  6. 2004: Farfesa a Fannin Sadarwar Al’adu da Kafafen Sadarwa (Media and Culture Communication), Jami’ar Bayero ta Kano.

Gogayyar Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Fitaccen masani ne shi a harkar ilimi, rubuce-rubuce da kuma karantarwa; ayyukan da ya kuma ɗauki shekaru arba’in cif

(1979 – 2019) yana yi. Tun fitarsa daga jami’a a shekarar 1979 ya fara karantarwa a matakin bautar ƙasa a Makarantar ‘Yanmata ta Ekwerazu (Ekwerazu Girls Secondary School, Umoarkrika, Imo) a Jahar Imo a Najeriya, inda ya karantar har zuwa 1980. Ya shiga karantarwa a Jami’ar Bayero a shekarar 1981, aikin da yake ciki har zuwa yau ɗin nan a matsayinsa na

Mataimakin Shugaban Buɗaɗɗiyar Jami’ar Najeriya (NOUN).[1]

Maluntar Ƙasa-da-Ƙasa[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan zamowar Farfesa Abdallah Uba Adamu malami a Jami’ar Bayero ta Kano, to kuma ya zama Maziyarcin Malami (Visiting Lecturer) a wasu jami’o’in ciki da wajen Najeriya. Kaɗan daga cikin su sun haɗa da:

  • 1992: Jami’ar California da ke Berkely ta ƙasar Amurka.
  • 2004: Jami’ar Köln da ke ƙasar Germany.
  • 2006: Jami’ar London, da ke London.
  • 2007: Kwalejin Barnard ta Jami’ar Columbia da ke New York, a ƙasar Amurka.
  • 2009: Jami’ar Basel da ke ƙasar Switzerland.
  • 2010: Jami’ar Florida da ke ƙasar Amurka.
  • 2012: Jami’ar Warsaw da ke ƙasar Poland.
  • 2015: Jami’ar Jahar Rutgers (Rutgers State University) da ke New Jersey ta ƙasar Amurka.[2]

Mataimakin Shugaban Jami’a[gyara sashe | gyara masomin]

Farfesa Abdallah Uba Adamu ya zama mataimakin Buɗaɗɗiyar Jami’ar Ƙasa ta Najeriya wato Vice Chancellor a Turance, a shekarar 2016. Muƙamin da yake kawo yanzu (2019).[2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 National Open University (2019). Professor Abdalla Uba Adamu. An Kuma ciro daga shafin:http://nou.edu.ng/officers/professor-abdalla-uba-adamu-0 Archived 2020-01-05 at the Wayback Machine
  2. 2.0 2.1 2.2 Bayero University Kano (2019). Abdalla U Adamu _ Bayero University, Kano- Academia.edu. An ciro daga shafin:https://buk.academia.edu/AbdallaAdamu
  3. 3.0 3.1 Adamu A. U (Babu shekarar wallafa). Abdalla Uba Adamu Full CV. An ciro daga shafin: https://auadamu.com/index.php/biography/6-au-adamu-ngr-full-cv-nov-2015-3