Filin jirgin saman Ajaokuta

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Filin jirgin saman Ajaokuta
Bayanai
Iri Yawon bude ido, Sufuri, flight (en) Fassara, cargo (en) Fassara, kamfani da filin jirgin sama
Ƙasa Najeriya
Aiki
Bangare na Afirka, Najeriya, Jihar Kogi da Ajaokuta
Mamallaki Filin jirgin saman Ajaokuta

Filin jirgin saman Ajaokuta ko Filin Jirgin saman Ajaokuta filin jirgin sama ne mai nisan kilomita 22 kudu maso yammacin Ajaokuta, wani gari a jihar Kogi a Najeriya.[1]

Sabon abu game da Filin jirgin[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 2021 majalisar dokokin ƙasa ƙarƙashin shugaban majalisar dattawa ta amince da ƙudirin gyaran wasu filayen jiragen sama a Najeriya; a cikin kasafin kudin Najeriya na 2022 filin jirgin saman Ajaokuta na cikin jerin filayen jiragen sama guda takwas da aka jera don gyarawa da haɓakawa. An fara wannan aikin ne don samar da ƙarin kuɗi da kuɗaɗen shiga daga filin jirgin saman Ajaokuta. Haka kuma na zirga-zirga da safarar kayan masarufi, ciki da wajen waje na ajaokuta da ƙarfe a jihar kogi.

Bayanai[gyara sashe | gyara masomin]

Filin jirgin saman yana a jihar Kogi a adogo a cikin garin ajaokuta ɗaya daga cikin masana'antu a jihar kogi, kamar yadda binciken ya nuna filin jirgin yana da Latitude na (7° 27' 15.59" N) da Longitude na (6° 27' 23.99" E.).Filin jirgin saman manyan jirage basa tashi a cikin shi, kawai ƙananun jirage ne kamar helikopta. Kuma akwai wasu filin jirgin saman kusa da kusa da filin jirgin. Irin su filin jirgin saman Lokoja mai tazarar kilomita 40, filin jirgin Akure mai tazarar kilomita 130 daga filin jirgin.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]