Jump to content

Gwanki

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Gwanki


Wuri
Map
 12°10′01″N 8°03′01″E / 12.166925°N 8.050312°E / 12.166925; 8.050312
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin Najeriyajihar Kano
tsaunin garin Gwanki
baban masslancin garin gwanki

Gwanki, Wani kauye ne dake Arewa Maso Yammacin jihar Kano. Garin na Gwanki yana a Karamar Hukumar Bagwai ta jihar Kano, wanda ke ƙarƙashin dagacin garin Gogori. Gwanki ta rabu har zuwa masu unguwanni uku. Unguwa ta farko ita ce Gwanki Babba, ta biyu Gwankin katoge, sai kuma kashi na uku wato Gwankin Dan Kwari sannan akarkashi kowace Gwanki akwai wasu kamar Gwanki babba akwai Gwankin makera da Kuma Gwanki unguwar Dole,da unguwar kwal,Sai gwankin katoge akarkashita akwai gwanki yaro akwai gwankin kufai dl, sai gwankin dankwari akarkashi ta akwai gwankin baban Mero dakuma wani yanki a cikin garin umbawa Wanda ƙarƙashin Gwanki Dan kwari yake wato. Ƙauye Gwanki na da al'umma masu yawa kuma masu son zaman lafiya da juna.[1]

Yanayi a kauyen Gwanki

[gyara sashe | gyara masomin]

Kamar ko'ina a Arewacin jihar Kano, kauyen Gwanki na da yanayi mai kyau na noma da kiwo, hakan ne ma ya sa ga baki dayan mutanen garin ba su da sana'a da tafi noma da kiwo.

Yanayin muhalli

[gyara sashe | gyara masomin]

Yanayin geographical co'ordination na kauyen Gwanki kamar haka, latitude, 11:35degreeN, da kuma Yanayin longtitude na 8,0333degreeE.

Kauyukan da suka zagaye kauyen Gwanki

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Gogori
  • Kodon Hayi
  • Kodon Kandas
  • Sare-sare
  • Umbawa
  • Dan Isa
  • Walawa
  • Rigar Are
  • Yakanawa

Al'ummar ƙauyen Gwanki Hausawa ne da Fulani, kuma addinin su shi ne musulunci. Kamar dai sauran garuruwan Jihar Kano.

  1. Garba, Abubakar (2002). State, City and Society: Processes of Urbanisation (in Turanci). Centre for Trans-Sahara[n] Studies.