Saratu Gidado

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Saratu Gidado
Rayuwa
Cikakken suna Saratu Gidado
Haihuwa Jihar Gombe, 17 ga Janairu, 1968
ƙasa Najeriya
Mutuwa jihar Kano, 9 ga Afirilu, 2024
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Jarumi
IMDb nm3885616
Headshot of Saratu Gidado Daso
saratu Gidado

Saratu Gidado (An haife ta 17 ga watan Janairu, 1968 zuwa 9 ga watan Afrilu, 2024), an haifi Saratu Gidado a unguwar Dan AGundi dake birnin Kano a ranar 17 ga watan Janairun 1968. Wacce aka fi sani da Daso, ‘yar wasan fina-finan Najeriya ce, a masana’antar fina-finan Kannywood. Daso ta fi fitowa a matsayin muguwa a fina-finan ta. Ta fara fitowa a fim a shekarar 2000 a fim ɗin Linzami Da Wuta, wanda kamfanin shirya fina-finai na Sarauniya Movies ta shirya.[1][2] Dagana kuma ta cigaba da fitowa a sauran finafinai kamar Nagari, Gidauniya, Mashi, da Sansani.[3] Ta tabbatar da cewa tana son taka rawar a matsayin Muguwar Mace, a shirin fim.[4]

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Saratu Gidado a Jihar kano dake Arewacin Najeriya. Ta yi makarantar firamare a Jihar Kano. Ita ce matar aure ta farko a masana'antar Kannywood.

Baya ga riko, an nada saratu Gidado a matsayin jami’ar hulda da jama’a (Jakadiya) ga Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a shekarar 2016.

Fina-finai[gyara sashe | gyara masomin]

Saratu Gidado ta shiga masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood a shekarar 2000, kuma ta fito cikin fina-finai sama da 100.[5]

Take Shekara
Yar Mai Ganye
Cudanya
Nagari
Sansani
Mashi
Fil'azal
Gidauniya
Gidan Iko
Jakar Magori
Mazan Baci
Mazan Fama
Rintsin Kauna
Shelah
Uwar Kudi
Yammaci
Daham 2005
Sammeha 2012
Gani Gaka 2013
Ibro Ba Sulhu 2014
Akwai Hanya 2016
Ba Tabbas 2017

Game da mutuwar ta[gyara sashe | gyara masomin]

'Yan uwan Daso da suka zanta da kafofin watsa labarai sun tabbatar cewa mutuwar fuju'a ce ta riske ta daga kwanciya bacci gabanin tayi sahur.

Sai dai wata yar uwan ta Zeenaru Muhammad Gidado ta zanta da Aminiya ta ce marigayiyar tayi fama da mura mai karfin gaske har ta kai numfashin ta yana sarkewa [6].

Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Gidado ta rasu ranar 9 ga watan Afrilu, 2024, wanda yayi daidai da watan Ramadan Ashirin da tara ga watan, ta yi sahur kafin ta kwanta barci, ta rasu tana barci tana da shekaru 56, an yi jana’izarta bayan Sallan La'sar kamar yadda addinin Musulunci ya koyar.[7] Sarkin Kano Malam Aminu Ado Bayero ya samu damar halartar jana'izar nata da wasu sauran manyan mutane da 'yan film.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Matazu, Hafsah Abubakar (23 March 2019). "5 Kannywood veterans still on screen". Daily Trust. Archived from the original on 9 October 2019. Retrieved 9 October 2019.
  2. "I'm the only married woman that is still into acting – Daso". Blueprint. Retrieved 9 October 2019. Unknown parameter |hidate= ignored (help)
  3. "TOP 10 NORTHERN ACTRESSES". Modern Ghana (in Turanci). Retrieved 9 October 2019.
  4. Blueprint (2021-08-27). "Why I like playing role of wicked women – Daso". Blueprint Newspapers (in Turanci). Retrieved 2022-07-23.
  5. "Saratu Gidado [HausaFilms.TV - Kannywood, Fina-finai, Hausa Movies, TV and Celebrities]". hausafilms.tv. Hausa Tv. Retrieved 9 October 2019.
  6. https://aminiya.ng/dalilin-mutuwar-daso-da-ta%C6%99aitaccen-tarihinta/
  7. Bahara, Hafsat Bello (2024-04-09). "JUST-IN: Veteran Kannywood Actress Saratu Daso Is Dead" (in Turanci). Retrieved 2024-04-09.