Abubakar Imam
An taskan ce wannan muƙalar a cikin jerin Muƙaloli_masu_kyau a Hausa Wikipedia
Ana sa ran wata rana wannan muƙalar zata kasance a Babban Shafin Muƙalar mu a yau |
Abubakar Imam | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Kagara, 1911 |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Hausa |
Mutuwa | 1981 |
Karatu | |
Makaranta | UCL Institute of Education (en) |
Harsuna |
Turanci Hausa Larabci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan jarida da marubuci |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Jam'iyar siyasa | Northern People's Congress (en) |
Alhaji Abubakar ImamAbubakar Imam (Taimako·bayani) O.B.E, C.O.N, L.L.D, (Hon.) N.N.M.C, shahararren marubucin Hausa ne wanda ya wallafa littattafan Hausa da dama, cikinsu akwai irinsu Magana Jari Ce, Ruwan Bagaja da sauransu. Marubucin ya sama shahara a Duniyar Nazarin Harshen Hausa. Ya zamo edita na farko a gidan jaridar Arewa, Gaskiya Ta Fi Kwabo yanzu haka a na nazarin wallafe-wallafen da ya yi a manya da kananan makarantu a Nijeriya. Abubakar Imam shine marubucin littattafan Hausa na farko-farko a karni na (20), a tsakanin watan Afrilu zuwa watan Agusta na shekara ta alif dari tara da talatin da hudu (1934).[1]
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Alhaji Dr. Abubakar Imam, O.B.E; C.O.N.; LL.D (Hon.) N.N.M.C. a Cikin shekara ta alif dari tara da sha daya (1911), a cikin garin Kagara sa'an nan tana cikin lardin Kontagora, yanzu kuwa Jihar Neja. [2]Ya yi makarantar horarwa wato Katsina Training College, kuma ya kama aikin malanta a Makarantar Midil ta Katsina a shekara ta alif (1932), Yana da shekara (22), ya rubuta littafin hikaya na 'Ruwan Bagaja Archived 2015-10-03 at the Wayback Machine'. Ganin kwazonsa wajen kago labari mai ma'ana ya sa Dr. R.M. East, shugaban Ofishin Ta'alifi na Zariya, ya roki a bada shi aro daga Katsina ya yi aikin rubuce-rubuce a Zariya. A zamansa na Zariya ne Abubakar Imam ya wallafa littafin gajerun kagaggun labarai na Magana Jari Ce (1-3), Ikon Allah (1-5) da Tafiya Mabudin Ilimi.[3] Nothern Privinces Newsheet ne kamfani na farko da ke buga rubutun ajami a kasar Hausa, wanda aka kafa a Kano.[4] Daga baya kuma an kafa Nothern Nigeria Publishing Company (NNPC) wadanda suke wallafa litattafai a cikin Harshen Hausa.[5] Sannan aka kafa gidan jarida ta farko mai suna “Gaskiya Tafi Kwabo” Ma’ana “ Truth is Worth More Than a Penny” wacce aka kirkira a shekara ta (1939), wanda a lokacin Abubakar Imam shine mai kula da harkokin rubutu a kamfanin.[5]Abubakar Imam ne mutum na farko da ya fara wallafa littafin labarin Hausa a kasar Hausa mai suna “Ruwan Bagaja” a shekara ta (1934), [6]() a lokacin yana da shekara (23), sai Bello Kagara, wanda yaya ne ga Abubakar Imam,[7] wanda ya wallafa littafin Gandoki littafi mai shafi (45). Sai littafi mai suna “Idon Matambayi” na Muhammadu Gwarzo a shekara ta (1911 zuwa shekara ta 1971), Littafi na biyar shine “Jiki Magayi”, amman littafain Magana Jari ce tafi kowanne littafi karbuwa a karnin.
1- Ruwan Bagaja Abubakar Imam
2- Shaihu Umar Tafawa balewa
3- Idan Matambayi Muhammadu Gwarzo
4- Gandoki Bello Kagara
5- Jiki Magayi John Tafida da Rupert East
6- Magana Jari ce Abubakar Imam
Abubakar Imam yace ya dauke shi kimanin watanni shida yana rubuta littafin magana jari ce.[8][9] Yawancin labaran dake cikin littafin Magana Jari Ce ya samo ne daga labarun tatsuniya na Grimon, labarun larabawa da dan Indiya kuma kimanin labarai 80 ya samo su daga wasu littattafan da Rupert East ya ara mai,[10] shi kanshi Abubakar Imam Yace “shi kanshi Rupert East ya tattaro bayanai daga cikin littattafai daban-daban na turawa da tatsuniyan larabawa, domin yin amfani dasu a matsayin abun amfani na sharan fage”.[11] Magana Jari ce ta kasance babban littafin da tafi kowanne a jadawalin tsarin rubuta littafi ga Hausawa har ila yau.[12][13]
Ruwan Bagaja
[gyara sashe | gyara masomin]Ruwan Bagaja yana daya daga cikin shahararrun littafin da Abubakar Imam ya wallafa, littafin labarai ne a cikin labari, inda Alhaji Imam ke bada tarihin rayuwarsa da kansa. A littafin, yakan tara mutane yana basu labarinsa, su kuma suna jinsa. Labarin littafin ya kunshi inda Imam ke barin gida wajen neman Ruwan Bagaja domin neman ma wanda ya rike shi magani da kuma fitar dashi daga kunya. Daga bisani ya fita gida tun da kuruciyarsa inda yawo ya kai shi har Indiya, inda daga bisani ya dawo gida yana dan shekara arba'in.
Gyara Ruwan Bagaja
[gyara sashe | gyara masomin]Rupert East ya sanya gasar littattafai inda aka kai ‘Ruwan Bagaja’ don gyare-gyare a lokacin ta hanyan Katsina Middle School. A watan Aprilu 30th, shekarar 1934, Rupert East ya rubutawa Mr. Allen, Shugaban Makarantar Katsina Middle School ga Mallam Abubakar Imam, cewa suna godiya, da turo takardan Abubakar Imam da aka yi zuwa wajen su amma a wannan lokacin ba za su iya wallafa littafin ba domin littafin ya ruwaito labarinsa da yawa daga wasu littattafan kuma babu wasu canje canje. Duk da cewa littafin ya tsaru kuma sun yabe shi. Inda ya bashi shawaran da ya rubuta wasu labaran da kanshi domin a sanya su domin samun daman wallafa littafin da sunanshi shi Abubakar Imam. A watan Augusta East ya sake rubutawa Abubakar Imam wasika inda yake sanar dashi cewa sun kusa gama gyare-gyaren littafin nasa a cikin littafin.[14]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Ya fara nazarin littafin shi wanda yasa masa suna ‘RUWAN BAGAJA’ a wannar shekaran. Inda shekara mai zuwa baturen mulkin mallaka ’Rupert East’ ya sanya gasan littattafai inda aka kai Ruwan Bagaja domin gyare-gyare. Masana Harshen Hausa sun tabbatar da cewar har ya zuwa yanzu babu wani marubuci da ya baiwa Adabin Hausa gudunmowa ta musamman fiye da Alhaji Abubakar Imam, domin kasancewarsa marubuci mai cikakkiyar basira da fasahar shirya labarai iri daban-daban. Duba da muhimmancinsa ne ma, ya sa masana su ka sanya talifinsa cikin jadawalin darussan Hausa a Makarantun Sakandire da kuma Jami'o'i. Wadansu littatafan da Alhaji Abubakar Imam ya rubuta sun hada da Tarihin Annabi (S.A.W) Kammalalle da kuma Karamin Sani Kukumi.Hakika, Alhaji Abubakar Imam yana sahun gaba a manyan taurarin adabin Hausa Kuma wanda Har ila yau bashida tamka a Fannin Kaga Labarai[14]
Nagarta
[gyara sashe | gyara masomin]Duba ga irin gudunmuwa da ya bayar ga Tallafi da Aikin Jarida, Masarautar Burtaniya ta girmama Alhaji Abubakar Imam da lambar girma ta O.B.E, Order of British Empire. Daga bisani kuma gwamnatin Nijeriya ta girmama shi da tata lambar makamanciyar O.B.E, wato C.O.N. Yanzu haka gwamnatin Jihar Kano ta sanya sunansa a Babban Asibitin Kula da ma su Yoyon Fitsari, wato Abubakar Imam Urology Hospital, da ke Birnin Kano.
Shafin Waje
[gyara sashe | gyara masomin]Bibiliyo
[gyara sashe | gyara masomin]- Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute. ISBN 978-1-4744-6829-9. OCLC 648578425.
- Imam, Abubakar (1977). Magana Jari Ce Yaro, Bada Kudi a Gaya maka (in Hausa) (Littafi Na Uku ed.). ZARIA: NORTHERN NIGERIAN PUBLISHING COMPANY.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Salisu, Ahmed (1 September 2014). "Tarihin Alhaji Abubakar Imam". DW Hausa. Retrieved 25 May 2021.
- ↑ Abba Musa (2009-02-15). "ABB MUSA: Gundarin Tarihin Alhaji Dr. Abubakar Imam Kagara". abbamusa.wordpress.com. Archived from the original on 2012-07-24. Retrieved 24 June 2010.
- ↑ Bashir Ahmad (2011-07-13). "DANDALIN BASHIR AHMAD: Takaitaccen Tarihin Dr. Abubakar Imam". Dandalinbashir.blogspot.com. Retrieved 2013-11-08.
- ↑ Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute. p.12
- ↑ 5.0 5.1 Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute. p.13
- ↑ Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute. p.20-21
- ↑ Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute. p.26
- ↑ Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute. p.33
- ↑ (mora1989)(p26)
- ↑ pilaszawicz (1985)(p222)
- ↑ mora (1987)(26)
- ↑ Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute. p.34
- ↑ Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute. p.56-59
- ↑ 14.0 14.1 https://dailytrust.com/abubakar-imam-forty-years-after/