Komadugu Yobe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Komadugu Yobe
General information
Tsawo 1,200 km
Labarin ƙasa
Map
Tsarin Daidaiton Labarin Kasa 12°39′06″N 10°38′50″E / 12.6517°N 10.6472°E / 12.6517; 10.6472
Kasa Nijar da Najeriya
Hydrography (en) Fassara
Watershed area (en) Fassara 148,000 km²
Ruwan ruwa Chad Basin (en) Fassara
River mouth (en) Fassara Tabkin Chadi
Dauka yankin na kogin Yobe
Kogin Yobe a cikin shekarar 1900

Kogin Yobe, wanda kuma aka san shi da Komadougou Yobe ko Komadougou-Yobe a harshen Faransa, wani kogi ne a Yammacin Afirka wanda ke kwarara zuwa tafkin Chadi ta hanyar Najeriya da Nijar . Mahadar wannan kogin ya hada da Kogin Hadejia, da Kogin Jama'are [1] da kuma Kogin Komadugu Gana. Kogin ya zama wani sashi na iyakar ƙasa tsakanin Nijar da Najeriya.[2]

Akwai damuwa game da sauye-sauye a kan gudanar ruwan kogin, dangane da tattalin arziki da kuma tsabtace muhallin kogin, a halin yanzu shi ne Dam din Tiga a cikin jihar Kano, tare da shirin tattaunawa game da Dam din Kafin Zaki a cikin jihar Bauchi. [3]

Manyan biranen dake kusa da kogin sun hada da Gashua, Geidam, da Damasak a Najeriya, da Diffa a Jamhuriyar Nijar.

Dubi kuma[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Hadejia". Encyclopædia Britannica Online. Encyclopædia Britannica, Inc. Retrieved 2007-05-13.
  2. "Niger". Encyclopædia Britannica Online. Encyclopædia Britannica, Inc. Retrieved 2007-05-13.
  3. Kole Ahmed Shettima. "Dam Politics in Northern Nigeria: The Case of the Kafin Zaki Dam". York University, Canada. Retrieved 2009-10-01.

Mahadan kasa: 12°39′06″N 10°38′50″E / 12.65167°N 10.64722°E / 12.65167; 10.64722