Koko (abinci)
Appearance
(an turo daga Ko'ko)
| abinsha |

Koko dai abinci ne mai ruwa-ruwa da akan dama shi da ƙullun gero ko dawa ko kuma masara. Koko abinci ne da aka fi shan shi da safe ko da yamma. Koko an fi haɗa shi da ƙosai ko burodi ko gida wajen shan shi. Sannan akan sanya wa koko sukari ga mai buƙata duk da wasu ba su buƙatar sukarin [1]
Sinadaran yin koko
[gyara sashe | gyara masomin]Gero ko kuma dawa sannan ana shan shi da sikari, kosai, ko kuli-kuli.
yadda aka haɗa koko
[gyara sashe | gyara masomin]Za a dama kullun koko da ruwan sanyi Sannan a kawo tafasasshen ruwan zafi a zuba sai arufe jim kaɗan sai abuɗe a motsa