Shekarau Angyu
Shi ne Aku-Uka na 27. Sarki ne mai daraja ta daya, kuma shugaban majalisar sarakunan Jahar Taraba (chairman Taraba council of chiefs). Shi ne (Dr.) Shekarau Angyu Masa Ibi Kuvyo II, CFR, Aku-Uka na Wukari. Shi ne na 27 a jerin Aku-Uka da aka yi a tarihin wannan sarauta ta Aku-Uka. Sannan kuma shi ne mafi dadewa a kan karagar mulki. Mutum ne shi mai nagarta. Yana da hakuri, jajircewa, kwazon wajen aiki, son jama’a, da kuma iya zama da jama’a. Mutum ne mai matukar son ci gaba a dukkan abin da ya saka a gabansa. Yana da gogayyar rayuwar aiki tun zamanin turawa har zuwa yau din nan; abin nufi shi ne cewa ya yi aiki da Turawa tun kafin samun ‘yancin kan Najeriya har zuwa bayan samun ‘yanci. Shekarau Angyu, direban mota ne, dankasuwa, sannan kuma basarake. Dukkan wadannan abubuwa da aka ambata, su ne burikan rayuwarsa, kuma Allah cikin ikonsa ya cika masa su daya bayan daya kamar yadda ya ambata a lokacin da yake amsa tambayar malaminsa na makaranta a lokacin da yake karatu a garin LMakarantun rin Ibi, cewa, “so na ke na zama direba, dankasuwa sannan kuma sarki”. Dan wannan rubutu da mai karatu zai karanta, taba-ka-lashe ne game da kuma rayuwar wannan managarcin sarki wanda ya sauya tarihin Jukunawa da tsohuwar daular Kwararrafa a wannan zamani da mu ke ciki. Dr. Shekarau Angyu Masa Ibi Kuvyo II,
Sarki ne mai daraja ta daya, kuma shugaban majalisar sarakunan jahar Taraba (chairman Taraba council of chiefs).[1]
Haihuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Shekarau a ranar Lahadi 18 ga watan Afirilu na shekarar 1937; wato yau yana da shekaru 80 (1937 – 2017) cur a duniya. Shi ɗa ne ga Ashumanu II Angyu Masa Ibi; Aku-Uka na 22, wanda ya yi zamani 1940 – 1945. Sunan mahaifiyarsa Buvini Awudu. Ya fito daga zuriyar Ba- gya; daya daga cikin gidajen sarautar Wukari. Wannan suna nasa Shekarau, suna ne da ya samo asali daga Hausa. A al’adar Hausa, idan mace mai ciki ta haura wata tara bata haihu ba, to akan kira abin da ta haifa da suna shekarau idan namiji ne, mace kuma a ce da ita shekara. Wato ana nufin mutumin da ya shekara a ciki. Sunansa na yare kuma shi ne Agbunshu. Kenan, sunansa ya zama Shekarau Agbunshu.[2]
Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]1. 1950 – 1954: Makarantar Elimantare ta Wukari (Wukari Elementary School). 2. 1954 – 1957: Babbar Makarantar Mishan ta Lapwe da ke Ibi (Missionary Senior School Lapwe). Gogayyar Aiki 1. 1958 – 1960: Ya yi aiki da Hukumar Gargajiya ta Wukari a matsayin Jami’in rarraba wasiku (mail officer), daga baya aka dauka matsayinsa zuwa jami’in sufuri; wato babban direba kenan (transport officer), sauyin da ya cika masa burinsa na Farko na son zama direba. Ayyukansa a wannan matsayi sun hada da tabbatar da lafiyar dukkan ababen sufuri mallakin wannan hukuma, da kuma tabbatar da cewa an bayar da su ga wanda ya dace a duk lokacin da bukatar amfani da su ta taso, sannan kuma a halin da za su iya amfanuwa. 2. 1960 – 1962: Jami’in Taimako (personal assistance) ga ‘executive officer’ na ma’aikatar kula da lafiyar dabbobi (ministry of animal health) na gwamnatin arewa da ke Kaduna a wancan lokacin Dr. Samuel Ɗanjuma A. Gani. 3. 1962 – 1963: Jami’in Taimako (personal assistance) a ofishin sakataren mulki (parliamentary secretary) na gwamnatin arewa da ke Kaduna a wancan lokacin, Ambasada Jolly Tanko Yusuf. 4. 1963 – 1966: Jami’in Taimako (personal assistance) a ofishin shugaban ma’aikatar wutar lantarki ta Najeriya (Electricity Corporation of Nigeria), Malam Ibrahim Sangari Usman. 5. 1966 – 1976: Jami’in Ciniki (sales manager) a gidan man-fetur na Makurdi (Texaco filing station, Makode). Wannan sabon ci gaba da kuma sauyin aiki daga ma’aikatar gwamnati zuwa kamfani mai zaman kansa shi ne abin da ya tabbatar wada Shekarau burinsa na biyu na son zama dan kasuwa. Tun da farko, gaskiya da rikon amana su ne halayen da suka shugabansa a ma’aikatar wutar lantarki ya dora shi a wannan babban matsayi a kuma wannan sabon gidan mai nasa. Zaman shekarau a wannan kamfani ya kafa kamfanin, dan abin da ya yi ya fi karfin a ce ya samar da ci gaba. Ya rike wannan gidan mai tun yana guda daya tilo a lokacin da aka bude shi har ya hayayyafa tare kuma da karin samar da wasu sababbin abubuwan yi da ba sayar da man-fetur ba. Daga cikin irin wadannan ayyuka da shekarau ya shigo da su wannan kamfani akwai sabis na mota, sayar da wasu kayayyaki, yin faci da sauran su.
Sarauta
[gyara sashe | gyara masomin]A ranar 28 ga watan Agusta na shekarar 1976, aka bayar da sanarwar nadin Shekarau Angyu a matsayin sabon Aku-Uka na Wukari. Nadin da ya saka shi zamowa Aku-Uka na 27 a garin na Wukari. Wannan mataki da ya taka a rayuwa, shi ne abin da ya cika masa burinsa na karshe kamar yadda ya ambata a shekaru 20 da suka gabata, cewa, yana so ya zama direba, dan kasuwa, daga karshe kuma ya zama sarki. Hakkin wannan nadi na Dr. Shekarau Angyu Masa Ibi Kuvyo II, ya samu karbuwa tare kuma da amincewar ‘yan majalisar sarki kuma masu Zaben sabon sarki guda hudu, da kuma yarjewar iyalan gidajen sarauta guda biyu; Ba-gya(Kuvyo) da kuma Bama. Tun da [3] ga wannan lokaci zuwa yau (1976 – 2017), Dr. Shekarau Angyu shi ne Aku-Uka na Wukari. Wato kenan, zuwa yau (2017), yana da shekaru 41 a kan karagar mulkin Jukunawa mai helikwata a Wukari. Sannan kuma shi ne Aku-Uka mafi dadewa a kan karagar mulki.
Gudunmawa
[gyara sashe | gyara masomin]Masu iya magana sun ce, mai kamar zuwa akan aika, a wani fadi kuma suka ce kowa ma ya yi rawa bare dan makada. Hakika wannan maganganu haka suke. Dr. Shekarau Angyu Masa Ibi Kuvyo II, mutum ne da ya samu horo tun daga tushe na yi wa jama’a hidima, sannan kuma aka yi gam-da-katar cewa mutum ne mai shawa’ar yin hakan. Wato zani ce ta taras da mu je mu. Gudunmawa da Dr. Shekarau ya bayar a wannan gari sannan kuma cibiyar sabuwar Daular Kwararrafa, tana da tarin yawan gaske. Gari ne da ya same shi a matsayin karamin gari, a yau kuma ya maishe shi katafariyar alkariya mai kusan dukkan abubuwan da birane ke bukata na kayan more rayuwa. Saboda haka sai dai mu dan tsakuro mu rubuta kamar haka: 1. Fannin Raya Al’adu da farfado da daular Kwararrafa: Hakika Dr. Shekarau Angyu Masa Ibi Kuvyo II, ya taka muhimmiyar rawa wajen sake raya al’adun Jukunawa da kuma farfaɗo da daular Kwararrafa. Tun farkon hawansa mulki yake kokari a wannan fannin har ta kai a yau ana iya tunawa da waccar tsohuwar daula ta Kwararrafa tare kuma da ganin al’adu da kyawawan halayen Jukunawa na son zaman lafiya, karbar baki da sauran su. Tabbas a yau duniya tana iya banbance tsohuwar suturar Jukunawa, salon rawarsu ta gargajiya, da kuma ta zamani. 2. Abubuwan More Rayuwa: A wannan fanni na wadata Wukari da ababen more rayuwa, kusan ana iya cewa dukkan wani abin more rayuwa da ake bukatar sa a alkarya, to akwai shi a wannan gari na Wukari, kamawa tun daga layukan tarho na dauri da na zamani, cibiyar aika wasiku, tituna, wutar lantarki, kasuwannin zamani, ababen hawa, gidajen man-fetur, manya da kananan otel, gidajen saukar baki, da sauran abubuwan more rayuwa rankacakam. 3. Ilimi: Ilimi gishirin zaman duniya, garin Wukari, gari ne da ke cike da makarantu kamawa tun daga firamare har zuwa jami’o’i; ba fa jami’a ba, a’a, jami’o’i. Saboda akwai jami’o’i guda biyu a garin Wukari, daya ta gwamnatin tarayya, dayar kuma mai zaman kanta wacce ake kira Kwararrafa University. Makarantun.firamare, sikandire da kwalejoji ma kuma duk akwai su birijik a garin na Wukari.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Adamu Ɗ. A. (2016). Shekarau Angyu Masa-Ibi, An Autobiography of the 24th Aku-Uka, as Told to Danjuma A. Adamu.An buga a Able Productions tare da haxinGuiwar Animation Books.
- ↑ Oluyede I.O. (1996). Shaped by Destiny, A Biography of (Dr.) Shekarau Angyu Masa-Ibi, Kuvyo II, The Aku Uka of Wukari. University of Ilorin.
- ↑ Tattaunawa da (Dr.) Shekarau Angyu, Masa-Ibi, Kuvyo II, Aku Uka na Wukari, a ranar Asabar 19/08/2017, a fadarsa da ke Wukari