Jump to content

Abubakar Ladan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Abubakar ladan zaria)
Abubakar Ladan
Rayuwa
Mutuwa 2014
Sana'a

Abubakar Ladan ya kasance fitaccen mai waƙoƙin da suka shafi kishin kai da dogaro da kai, musamman a nahiyar Afrika.[1]

Farakon rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Ladan a shekarar 1935 a unguwar Ƙwarbai dake birnin Zariya a jihar Kaduna, arewacin Najeriya. Bayan shekara biyar da haihuwan sa an saka shi a makarantar allo. Bayan ya sauke karatun Qur'ani a shekara ta (1946), ya shiga makarantar share fagen shiga Elementare in da kuma ya kammala a shekara ta (1950), daga nan kuma ya shiga makarantar middle ta Zariya da ake kira Alhudahuda. Ashekara ta (1954 )Abubakar Ladan ya kammala makarantar Alhudahuda, sai kuma ya fara aiki agarin Malumfashi. Daga nan kuma ya fara aikin malamin dabbobi ko vetanariya, inda kuma yake fannin bincike akan ƙudan tsando. Bayan ya bar aikin vetanariya, ya kuma fara aiki a matsayin malamin kula da ingancin fatu da ake sasarafawa akanfanoni a Kano. Alhaji Abubakar Ladan ya fara waken Hausa ne a lokacin da ya fara karance karancen wakokin Hausa irin nasu Sa'adu Zungur da Mu'azu Haɗeja da kuma wani mawakin Larabci na Sudan mai suna Abdulkarem Al-kabirun. Abubakar Ladan ya kai ziyara ƙkasashen Afirka da dama da suka haɗa kuma da Sudan da Maroko da Habasha da Somaliya da su Kwango da Nijer da Iritiriya. Yanzu haka dai Alhaji Abubakar Ladan Zariya yana da 'ya'ya goma dakuma matan aure. A zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa Alhaji Shehu Shagari an ba shi lambar yabo ta MON. A shekara ta( 2014 ),tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya ba shi lambar yabo ta OON.

Mawakin mai shekaru( 79), ya rasu ne a gidansa da ke Zaria kuma an yi jana'izarsa a birnin Zariyan na jihar Kaduna bayan doguwar jinya Allah yajikansa da rahma.

  1. "Why I'm getting rotten at 74, Abubakar Ladan Zaria, a famous Housa Poet". Daily Trust. Retrieved 13 October 2021.