Ahmad D Prince

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Ahmad D Prince jarumi ne a masana'antar fim Amma yayi shekaru 4 a masana antar jarumi kuma mawaki ne bafullatani kyakkyawa. Ya fara fim a shekarar 2018[1]

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Cikakken sunan sa shine Ahmad Muhammad Umar wanda akafi sani da D Prince. An haife shi a ranar 1 ga watan Janairu shekara 1998, an haife shi a wata unguwa Mai suna Damboa road, kasance war su Fulani sunyi zaman guru daban daban. Asalin su Yan Sudan ne mahaifiyar su ta shigo dasu nijeriya suka zama Yan kasa. Yayi karatun firamare a Karamar hukumar mafa, yayi karatun sakandiri a balabirim, ya karasa karatun sakandiri a "Success Secondary School" bolari. Yayi karatun kwamfuta a makarantar kwamfuta dake kusa da gidan waya na Maiduguri, yayi karatun satifiket a Arabic. Daga Nan yayi karatun difloma a goni college of Islamic studies . A halin yanzun Kuma Yana karatun digiri ta onlayn a kasar Uganda ya kusa gamawa.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://fimmagazine.com/gwagwarmayar-jarumi-mawa%C6%99i-ahmad-d-prince-a-kannywood/