Aryeetey Andrew Nii

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Aryeetey Andrew Nii BSc, MS, (an haifeshi ranar 18 ga watan Nuwamba, shekara ta alif ɗari tara da talatin da hudu1934A.C) a garin Accra dake Ghana. Andrew ya kasance masanin noma na kasar Ghana.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Yayi Makarantar Gwamnati dake accra, 1941-48, makarantar Achimota 1949-55, Jami'ar Ghana 1956-59, Jami'ar Illinois Chicagodak kasar Amurka 1966-68; jami'in noma a ma'aikatar noma 1959-64, babban jami'in noma, Yuli-Satumba 1964, jami'in bincike, tashar binciken noma, Kpong, Jami'ar Ghana, 1964-75, ya nada babban jami'in bincike, Yuni 1975.[1]

Aure[gyara sashe | gyara masomin]

Ya auri Martina Ofosu-Amaah a shekaran 1961. Sun haifi yara hudu (4) mata uku da kuma namiji daya.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Africa who's who (2nd ed ed.). London: Africa Books Ltd. 1991. ISBN 0-903274-17-5. OCLC 24954393. {{cite book}}: pp, 215-218