CIYARWA LOKACIN AZUMI

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bude baki lokacin azmi

Ma’anar kalmar "Azumi" a larabci Kamewa da barin wani abu Ma’anar Azumi a Shari’a Shi ne bautawa Allah ta hanyar kamewa daga cin abinci da abin sha da jima’i, tun daga hudowar alfijir har zuwa faduwar rana.[1]

CIYARWA[gyara sashe | gyara masomin]

Tarihi ya kawo labarin wata baiwar Allah da ta je wajen manzon Allah Annabi Muhammad (SAW) tana mai karar mijinta, cewa yana yawan gayyatar baki don yin buda baki a gidansu, kuma yawan aikin girki na wahalar da ita sosai. Manzon Allah (SAW) bai ce mata komai ba, haka ta tashi ta tafi. Bayan wani lokaci sai manzon Allah (SAW) ya kira mijin matar ya ce masa, "yau zan bakunci gidan ka." Mutumin ya tafi gida cikin farin ciki da murna, ya sanar da matarsa, wacce ita ma ta yi murna da haka. Matar nan ta tsaya ta shirya abinci mai dadi don tsimayin babban bakon su. Bayan isar manzon Allah (SAW) gidan ya zauna suka ci abinci da mai gidan, har ya yi musu addu'a. Da zai tafi sai yake gayawa mai gidan cewa, ya sanar da matarsa idan ya fita ta kalli kofar da ya bi. Haka kuwa aka yi, matar tana kallon kofar da manzon Allah (SAW) ya bi ya fita, sai ta ga wasu muggan kwari, kamar su kunama, macizai da wasu halittu masu ban tsoro suna fita suma daga gidan. Ba ta san lokacin da ta suma ba, saboda firgita. Yayin da ta je wajen manzon Allah (SAW) sai ya ce mata, "Abin da ke faruwa kenan a duk lokacin da wani bako ya zo gidanka ya ci abinci, yana fita ne da duk wani abu da zai iya cutar da rayuwar." Allah ya hore mana abin da za mu ciyar a cikin wannan wata mai alfarma.[2]

MANAZARTA[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://ha.wikipedia.org/wiki/Falalar_Azumi_Da_Hukuncinsa
  2. https://web.facebook.com/ZHausa/posts/nasiha-amfanin-ciyarwa-a-lokacin-azumidaga-lawal-walin-sulejatarihi-ya-kawo-laba/1837994879577039/?_rdc=1&_rdr