Capacitor

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
hotuna capacitor

Capacitor wani abune wanda yake ajiye wutan lantarki ta hade cajin lantarki a wuri biyu mafi kusa wadanda suke da kariya a tsakaninsu. Shi capacitor anfi saninshi da condenser "ma'ana canza zafi". dadin dadawa, shi capacitor wani abu ne da yake da kafafuwa guda biyu. Amfanin capacitor ya danganta ne da yanayin lantarkin da abu ke dauka. Sai dai yanayin daukar lantarki yana faruwa ne tsakanin abubuwa guda biyu masu daukar wutar lantarki a bisa madaukar kayan lantarki.

Shi capacitor yana da siffofi da kuma rabe rabe kala kala, ya danganta da wane irin aiki kake so da kuma wane irin capacitor kake bukata yayin kirkira. 

Mafi yawancin capacitors suna da karafa masu daukar wutar lantarki guda biyu wadanda wani abu da be daukar wuta ya rabasu. Shi wannan abun da be daukar wuta yana karama capacitor din caji. Abubuwan da basu daukar wuta sun kunshi gilashi, roba,da kuma katako.


Manazarta[1][gyara sashe | gyara masomin]

  1. Duff, Wilmer (1916) [1908]. A Text-Book of Physics (4th ed.). Philadelphia: P. Blakiston's Son & Co. p. 361. Retrieved 2016-12-01