Jump to content

Wikipedia:Game da Wikipedia Hausa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

An yi wannan zama na wayar da kan matasa game da harkokin aiwatar da Wikipedia ta Hausa a dakin taro na Chilla Suites da ke Nasarawa a Kano, a ranar Asabar 29/12/2018.

Zaman ya sami halartar al'umma daga sassa daban-daban, kama daga jami'o'i da makarantu da jarida da masu sha'awar rubuce-rubuce da sauran sassa na al'umma daban-daban.

An fara zaman ta hanyar gabatar da kai inda daga baya masu shirya taron a qarshen jagorancin Ammar da Aliyu suka ci gaba da gudanarwa.

Ana sa ran taron zai samar da hanyar bunqasa harkar rubutu da Hausa a Wikipedia gami da qara inganta harshen Hausa a fadin duniya.