Girma Ilimin Allah

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

GIRMAN ILMIN ALLAH


قال الله عز وجل في كتابه العزيز:

"ولو انما فى الأرض من شجرة اقلام والبحر يمده من بعده سبعة ابحر ما نفدت كلمات الله إن الله عزيز حكيم"

"Idan kuwa da a ce, duk bishiyar da take bayan kasa alkaluma ne, kogi kuma (ya zama tawadarsu), bayansa kuma akwai wasu kogunan guda bakwai kari a kansa to kalmomin na Allah ba za su kare ba. Lalle Allah Mabuwayi ne, Mai hikima." Luqmàn:27

A wannan aya Allah سبحانه وتعالى ya bayyana yalwa da fadin iliminsa marar iyaka. Ya buga misali don kusanto da ma'anar zuwa ga kwakwalen masu sauraro, da cewa, da a ce duk bishiyoyin da suke bayan kasa za a yi guntu-guntu da su a fere su su zama alkaluman rubutu, sannan duk wani teku a duniya a mayar da shi tawwada ta rubutu, sannan a kara da tekuna bakwai wadanda su ma za su zama karin tawwadar rubutu sannan duk a hada su a yi ta rubuta kalmomin Allah da su, to da ba su iya kare kalmominsa ba, domin ba su da iyaka ko makura, sai dai wadannan alkaluma da wannan tawwada su kare karkaf. Allah ya tabbatar da cewa lalle shi Mabuwayi ne babu mai iya rinjayar sa, mai hikima ne cikin duk maganganunsa da ayyukansa.

   سبحانك ما اعظمك يارب!!!

  Prof Muhammad Sani Umar Rlemo. Fayyataccen Bayani na Ma'anoni da Shiriyar Alqur'ani, vol:5, pg: 143

✍🏻 Umm Khaleel

                        🟤🟤🟤