Kalma me harshen damo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Kalma me harshen Damo[gyara sashe | gyara masomin]

Kalma me harshen damo shine kalma me ma'ana fiyeda guda ɗaya.[gyara sashe | gyara masomin]

Misali: Gari, dama da sauran su.

GARI[gyara sashe | gyara masomin]

Gari yana nufin wajen zama ta mutane, muhalli inda kuma mutane fiye da biyu seke yin rayuwar su, maraya kenan Wanda akwai gida je da gonakai da sauran su.

  • Azam ya tafi garin Hadeja.
  • Ranar asabar itace kasuwar Danchuwa.
  • Akwan tireloli dayawa agarin potiskum.

GARI[gyara sashe | gyara masomin]

GARI ita ce babbar riga ko bunjuma da ba haushe yake sakata ayayin biki, musamman ango, ko kuma wani babbar mutum medaraja acikin al'umma.

Wani lokacin ana kirantada malum-malum, amma  mafiyawa ana satane domin Kure adaka.

  • Ango yayi dainkin gari dashi da abokan sa.
  • Adamu baya son gari me aljuhu.

GARI[gyara sashe | gyara masomin]

GARI itace nikakken alkama, gero ko dayawa

Wanda ake amfani dashi wajen yin tuwa.

  • Bana garin masara tayi tsada sosai.
  • Injin gagale sun iya nika gari da laushi.

DAMA itama wanan kalmace me ma'ana fiyeda guda daya.[gyara sashe | gyara masomin]

DAMA[gyara sashe | gyara masomin]

Dama yana nufin samun sukuni, ko gamon katar.

misali:

  • Oranga yace "idan yasamu dama zai zo ku gaisa".
  • Salma taje har Kano amma bata samu damar ganin Ali Nuhu ba.

DAMA[gyara sashe | gyara masomin]

Itama wannan kalma ta dama tana nufin hada garin wani abu da ruwa, ko hada daskararren abu da wani narkakken abu.

Misali:

  • Fatima ta iya dama Fura da nono.
  • Aisha ta dama kunun Aduwa jiya.