Ƙofar Ƴanɗaka
Appearance
(an turo daga Kofar ‘Yandaka)
Kofar ‘Yandaka |
---|
Kofar Yandaka tana daga cikin Tsofuwar kofa a Jihar Katsina wadda aka gina a karni na Shabiyar (15).
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Ta samo asalin sunanta ne daga Basaraken Habe na garin ‘Yandaka da ke yammacin birnin jihar Katsina. Ta wannan kofar ce ‘Yandaka ke bi idan zai fita zuwa ‘Yandaka, ta nan ne kuma yake shiga in ya dawo Kofar ‘Yandaka ta yi makwabtaka da Gafai daga arewa; Masanawa daga gabas, tare da Marinar Kadabo da ‘Yantaba, duk daga gabas din.
A wajen kofar, akwai wasu wurare masu muhimmanci da za mu yi magana a kansu, kamar garin babbar Ruga da Filin Folo na Katsina, wadanda duk suke a yamma da kofar ‘Yandakan.