Katsina








Katsina Ƙaramar hukuma ce kuma babban birnin Jihar Katsina a Arewacin Najeriya. Katsina tana da nisan kilomita 260 km (160 mil) daga gabashin Birnin Sokoto, da kuma kilomita 135 Km (84 mil) daga Arewa Maso Yammacin Birnin Kano, tana kusa da iyakar ƙasar Nijar.
An ƙiyasta yawan mutanen dake cikin birnin Katsina a shekara ta 2016 da kimanin mutum 429,000.[1] Birnin akasarin mutanen birnin Musulmai ne daga ƙabilar Hausa da Fulani.
Tsohon shugaban ƙasan Najeriya Umaru Musa Yar'Adua ya kasance babban mutum ne daga Katsina.[2]
Gwamna mai ci na yanzu a Jihar Katsina shine
Umar Dikko Raɗɗa,[3] wanda aka rantsar a matsayin gwamnan jihar a ranar 29 ga watan mayu shekara ta 2023
Masarautar Katsina:
[gyara sashe | gyara masomin]Fadar Sarkin Katsina wanda akafi sani da "Gidan Korau" wani katafaren gini ne dake tsakiyar tsohon birnin na Katsina. Fadar ta kuma kasance muhimmin alama na daga al'adu, tarihi da kuma ɗabi'ar Katsinawa.
Kamar yadda tarihi ya nuna, Muhammadu Korau ya gina fadar a shekara ta 1348 CE, wanda ake tsammani cewa shi ne Sarkin musulmi na farko a Katsina. Wannan ne yasa ake kiran masarautar da Gidan Korau. Fadar na ɗaya daga cikin gidan sarauta mafi tsufa kuma na farko-farko, tare da masarautun Daura, Kano Zazzau. Masarutar zagaye take da ganuwa wato katangar gidan sarki wanda a yanzu babu ita. Ƙofar da ke isa zuwa masarautar ita ce 'Ƙofar Soro' sannan kuma ƙofar da ke bayan ta ita ce 'Ƙofar Bai' (babu ita a yanzu). Fadar sarkin a cikin masarautar wani ƙayataccen gini ne mai ƙirar salo na gargajiya.[4] Sarkin Katsina na yanzu shine Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, runbun ilimi daga dangin sarakunan Fulani.


Tarihi:
[gyara sashe | gyara masomin]Birnin na zagaye da ganuwa mai tsawon kilomita 21 (mil 13) wanda ake tsammani an gina ta a ƙarni na (1100).[5] Kafin zuwan addinin musulunci, jagorar Katsina na musamman shi ne Sarki, wanda yake fuskantar kisa a duk lokacin da aka same shi baya mulki yadda ya kamata. Daga ƙarni na 17 zuwa ƙarni na 18, Katsina ta kasance cibiyar kasuwanci na Ƙasar Hausa kuma ta zamo mafi girma daga cikin ƙasashen Hausa Bakwai. Fulani sun mamaye Ƙatsina a lokacin Jihadin Fulani a shekarar (1807). A shekarar 1903 ne, sarkin Katsina na lokacin Abubakar ɗan Ibrahim ya miƙa wuya ga mulkin Turawa, wadda ta ci gaba har zuwa samun 'yanci kai a shekarar 1960.

A lokacin kasuwancin yankunan kusa da Sahara na Afirka, birnin ya kasance mai albarka kuma muhimmin cibiyar kasuwanci, kuma ana ɗaukanta a matsayin mafi shahara ta fuskar cinikayya, kasuwanci da kuma baiwar sarrafe-sarrafe. Matafiyi ɗan kasar Jamus, Friedrich Hornemann ne bature na farko da ya fara isa birnin a ƙarni na 19.
Tarihin birnin dangane da ilimin boko ya samo asali ne tun daga farkon shekarun 1950, a yayin da aka gina makaranta ta matsakaita ta farko a arewacin Najeriya. Akwai manyan makarantu a yanzu wanda suka haɗa da jami'oi guda biyu, Jami'ar Umaru Musa Yar'adua da kuma ta 'yan kasuwa wato Jami'ar Al-Qalam Katsina; sannan kuma akwai politakanik wato Hassan Usman Katsina Polytechnic da kuma Federal College of Education, Katsina.Har wayau, birnin gida ne ga shahararren masallacin karni na 18 wato Hasumiyar Gobarau, hasumiya mai tsawon mita 15 (50 ft) wanda aka gina da laka da itacen dabino.
Al'amarin Boko Haram na 2020:
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin watan Disambar shekara na 2020, aka yi garkuwa da yara 300 ƴan makaranta a Ƙanƙara.[6] Amma daga bisani an maido da yara 344 mako ɗaya bayan hakan.[6] Ƙungiyar Boko Haram ta yi iƙirarin cewa ita ta aikata hakan, amma jami'ai sun nuna rashin amincewa da hakan kasancewa babu ƙungiyar Boko Haram a yankin.
kuma ita jahar katsina ta kasance cikin jerin jahohin nijeria guda talatin da shida 36.[7]
:
[gyara sashe | gyara masomin]- Jami'ar Umaru Musa yar,aduwa Katsina (UMYU).
- Jami'ar Al-Qalam Katsina ( a da Islamic University Katsina).
- Hassan Usman Katsina Polytechnic.
- Federal College of Education, Katsina.
- Katsina State Institute of Technology and Management (KTSITM).
- National Open University of Nigeria (NOUN).
- Cherish Enterprises Institute.
- Katsina Community College of Education [Affiliated to Ahmadu Bello University Zaria (A.B.U) suncais ground].
Hotunan Manyan wuraren garin Katsina tare da Makarantu:
[gyara sashe | gyara masomin]Manyan Wuraren Garin Katsina;
[gyara sashe | gyara masomin]-
Umaru Musa Yar'adua University Katsina
-
Katsina State Institute of Technology and Management
-
Hassan Usman Katsina Polytechnic
-
AlQalam University Katsina
-
Federal College of Education, Katsina State
Manyan Wuraren Garin Katsina;
[gyara sashe | gyara masomin]-
Kofar Gidan Sarkin Garin Katsina
-
Ofishin Biyan Haraji na Jihar Katsina
-
Steel Rolling Round About
-
Makarantar dake da Hasumiyar Gobarau
-
Asibitin Gwamnati na Jihar Katsina
-
Gidan Tarihin Jihar Katsina
-
Babbar Magudanar Ruwa dake Garin Katsina
-
Round About na Katsina
Labarin ƙasa:
[gyara sashe | gyara masomin]Yanayi;
[gyara sashe | gyara masomin]Dangane da rabe-raben yanayi na Koppen, Katsina ta faɗa acikin yanayi na zafi wato semi-arid climate, wanda ake rubuta wa a takaice da BSh a taswirorin yanayi na duniya.[8]

Ruwan sama;
[gyara sashe | gyara masomin]Akwai ƙarancin ruwan sama a birnin Katsina, babu rikodin na ruwa kwata kwata a tsakanin watannin Nuwamba zuwa March.
| S/N | Code | Shekaru | Junairu | Febreru | March | Aprelu | Mayu | Yuni | Yuli | Agusta | Satumba | Oktoba | Nuwamba | Disemba |
|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
| 1. | 65028 | 1990 | 0 | 0 | 0 | 0 | 29.9 | 57.9 | 198.8 | 220.2 | 34.7 | 0 | 0 | 0 |
| 2. | 65028 | 1991 | 0 | 0 | 10.8 | 12.2 | 73.5 | 58.8 | 71.5 | 109.7 | 21.1 | 1.4 | 0 | 0 |
| 3. | 65028 | 1992 | 0 | 0 | 0 | 0 | 33.6 | 19.9 | 89.3 | 119.4 | 70.7 | 0.2 | 0 | 0 |
| 4. | 65028 | 1993 | 0 | 0 | 0 | 0 | 4.5 | 42.3 | 69 | 94.5 | 51.7 | 0 | 0 | 0 |
| 5. | 65028 | 1994 | 0 | 0 | 0 | 3.1 | 12.3 | 42.3 | 107.9 | 174.2 | 113.1 | 20.3 | 0 | 0 |
| 6. | 65028 | 1995 | 0 | 0 | 0 | 10 | 30 | 70 | 80 | 120 | 80 | 10 | 0 | 0 |
| 7. | 65028 | 1996 | 0 | 0 | 0 | 0 | 42.6 | 44.5 | 38.1 | 66.8 | 67.8 | 0 | 0 | 0 |
| 8. | 65028 | 1997 | 0 | 0 | 7.2 | 9.5 | 89.5 | 30.4 | 91.1 | 153.7 | 56.5 | 8.3 | 0 | 0 |
| 9. | 65028 | 1998 | 0 | 0 | 0 | 10.1 | 11.4 | 43.4 | 114.1 | 116.6 | 135.2 | 0.8 | 0 | 0 |
| 10. | 65028 | 1999 | 0 | 0 | 0 | 0 | 4.2 | 22.4 | 149.2 | 89.8 | 132.3 | 18.4 | 0 | 0 |
| 11. | 65028 | 2000 | 0 | 0 | 0 | 0 | 1.6 | 106.8 | 299.9 | 160.2 | 62.1 | 45 | 0 | 0 |
| 12. | 65028 | 2001 | 0 | 0 | 0 | 16.9 | 83.9 | 110.8 | 176 | 240.9 | 70.6 | 0 | 0 | 0 |
| 13. | 65028 | 2002 | 0 | 0 | 0 | 0 | 2.9 | 141.3 | 170.4 | 71.3 | 199.1 | 9.8 | 0 | 0 |
| 14. | 65028 | 2003 | 0 | 0 | 0 | 4 | 52.8 | 57.2 | 118.2 | 275.5 | 75.1 | 16.4 | 0 | 0 |
| 15. | 65028 | 2004 | 0 | 0 | 0 | 0 | 74.9 | 151.2 | 161.1 | 268.8 | 42 | 0 | 0 | 0 |
| 16. | 65028 | 2005 | 0 | 0 | 0 | 14.8 | 18.4 | 83.2 | 173.7 | 216.1 | 194 | 50.4 | 0 | 0 |
| 17. | 65028 | 2006 | 0 | 0 | 0 | 0 | 26.1 | 69.9 | 170.9 | 314.9 | 129.7 | 15 | 0 | 0 |
| 18. | 65028 | 2007 | 0 | 0 | 0 | 6.2 | 84.9 | 135.2 | 117.4 | 314.9 | 45.5 | 0 | 0 | 0 |
| 19. | 65028 | 2008 | 0 | 0 | 0 | 16.6 | 8.5 | 63.3 | 182.9 | 213.9 | 67.7 | 4.2 | 0 | 0 |
| 20. | 65028 | 2009 | 0 | 0 | 0 | 0 | 95 | 57.9 | 96.5 | 123.3 | 38.3 | 29 | 0 | 0 |
| 21. | 65028 | 2010 | 0 | 0 | 0 | 85.6 | 8.1 | 118.8 | 226.1 | 448.9 | 76.6 | 48.6 | 0 | 0 |
| 22. | 65028 | 2011 | 0 | 0 | 0 | 0 | 38 | 149.2 | 116.6 | 180.6 | 67.3 | 8 | 0 | 0 |
| 23. | 65028 | 2012 | 0 | 0 | 0 | 0 | 59.5 | 135.2 | 117.4 | 314.9 | 129.7 | 15 | 0 | 0 |
| 24. | 65028 | 2013 | 0 | 0 | 0 | 42.4 | 36.7 | 103.2 | 89 | 274.7 | 107.6 | 10.2 | 0 | 0 |
| 25. | 65028 | 2014 | 0 | 0 | 0 | 0 | 38.1 | 39.5 | 178.9 | 178.7 | 46.3 | 0 | 0 | 0 |
| 26. | 65028 | 2015 | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 89.1 | 178.9 | 274.7 | 46.3 | 9 | 0 | 0 |
| 27. | 65028 | 2016 | 0 | 0 | 0 | 0 | 4.5 | 42.3 | 69 | 94.5 | 59.5 | 0 | 0 | 0 |
| 28. | 65028 | 2017 | 0 | 0 | 0 | 10.1 | 11.4 | 62 | 114.1 | 16.6 | 135.2 | 0.8 | 0 | 0 |
| 29. | 65028 | 2018 | 0 | 0 | 0 | 0 | 2.9 | 141.3 | 170.4 | 149.7 | 199.1 | 63.8 | 0 | 0 |
| 30. | 65028 | 2019 | 0 | 0 | 0 | 11.6 | 8.1 | 118.8 | 232.7 | 359.1 | 98.6 | 26.6 | 0 | 0 |
Tushe: Hukumar Kula da Yanayi, Katsina (NiMET) 2021.
Yanayin zafi ko sanyi;
[gyara sashe | gyara masomin]Yanayi na nufin yanayi na zafi ko kuwa yanayin sanyi na wuri
Zafi;
[gyara sashe | gyara masomin]Katsina na da yanayi na zafi sosai, tare da watan Aprelu a matsayin wata mafi zafi na kimanin 40.8 °C ko kuma 105.4 °F, tare da yanayi na matsakaicin zafi (31.4 °C or 88.5 °F) acikin watan December.[9]
| S/N | Code | Shekara | Junairu | Febrelu | March | Aprelu | Mayu | Juni | Juli | Augusta | Satumba | Oktoba | Nuwamba | December |
|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
| 1. | 65028 | 1985 | 31.7 | 29.7 | 36.5 | 36.5 | 38.6 | 35.9 | 31.6 | 31.3 | 33.2 | 35.5 | 33.9 | 28.2 |
| 2. | 65028 | 1986 | 38.9 | 34.7 | 37 | 40.2 | 39.2 | 37 | 31.5 | 31.4 | 32.2 | 35.4 | 33.3 | 37.4 |
| 3. | 65028 | 1987 | 30.4 | 33.6 | 36 | 37.6 | 40.1 | 36.6 | 35.1 | 32.6 | 34.4 | 35.7 | 34.1 | 30.1 |
| 4. | 65028 | 1988 | 28.4 | 32 | 36.7 | 39 | 39.2 | 35.3 | 31.9 | 29.5 | 31.9 | 34.3 | 33.7 | 28.5 |
| 5. | 65028 | 1989 | 26 | 28.4 | 35.2 | 39.3 | 38.3 | 36.2 | 32.4 | 30.9 | 32.6 | 33.6 | 33.6 | 29.6 |
| 6. | 65028 | 1990 | 32.2 | 30.1 | 33.5 | 39.9 | 38.1 | 36.7 | 31.7 | 31.4 | 33.9 | 36.7 | 35.5 | 34 |
| 7. | 65028 | 1991 | 29.4 | 35.9 | 35.9 | 39 | 35.3 | 35.1 | 31 | 30.5 | 34.4 | 36.4 | 33.3 | 28.9 |
| 8. | 65038 | 1992 | 29.1 | 30.1 | 36.4 | 39 | 36.5 | 35.6 | 31 | 30.3 | 32.4 | 35.7 | 31.5 | 30.2 |
| 9. | 65028 | 1993 | 36.5 | 32.5 | 36.5 | 39.3 | 39.3 | 36.5 | 33.3 | 31.5 | 33.1 | 36.9 | 35.5 | 29.5 |
| 10. | 65028 | 1994 | 29.5 | 31.6 | 38.2 | 38.7 | 38.9 | 35.4 | 31.8 | 29.5 | 31.4 | 34.1 | 32.3 | 27.4 |
| 11. | 65028 | 1995 | 27.7 | 31 | 38.1 | 38.8 | 38.3 | 36.1 | 32.9 | 30.9 | 32.6 | 35.4 | 32.2 | 31.7 |
| 12. | 65028 | 1996 | 32.1 | 34.8 | 37.6 | 39.3 | 38.3 | 34.5 | 33.6 | 30.3 | 32.3 | 35.3 | 31.2 | 31.8 |
| 13. | 65028 | 1997 | 31.3 | 28.5 | 34.8 | 38.3 | 36.5 | 35.1 | 32.4 | 31.7 | 33.6 | 36.5 | 35.6 | 30.4 |
| 14. | 65028 | 1998 | 29.4 | 33.5 | 33.9 | 40.2 | 39.3 | 35.6 | 32.1 | 30.8 | 31.6 | 34.9 | 34.9 | 30.6 |
| 15. | 65028 | 1999 | 30.8 | 34 | 39 | 39.5 | 39.3 | 38.1 | 31.7 | 29.5 | 31.4 | 33.4 | 33.2 | 29.7 |
| 16. | 65028 | 2000 | 31 | 28.6 | 35.2 | 40.5 | 39.6 | 35.3 | 31 | 31 | 32.9 | 33.8 | 33.8 | 29.6 |
| 17. | 65028 | 2001 | 29.3 | 30.4 | 36.9 | 38 | 37.8 | 34.3 | 31.3 | 30 | 32 | 34.8 | 33.6 | 31.9 |
| 18. | 65028 | 2002 | 26.3 | 31.6 | 37 | 39.8 | 40.8 | 36 | 32.5 | 31.1 | 32.2 | 32.4 | 33.8 | 31 |
| 19. | 65028 | 2003 | 34.7 | 35.3 | 39.6 | 39.4 | 34.4 | 35.6 | 31.3 | 30.8 | 32.8 | 33.8 | 33.5 | 31.7 |
| 20. | 65028 | 2004 | 32 | 29.9 | 40 | 39 | 36.5 | 32 | 30 | 33 | 36 | 34 | 33.9 | 31.9 |
| 21 | 65028 | 2005 | 13.4 | 19.4 | 22 | 24 | 25.2 | 24.2 | 22.7 | 21.6 | 22.3 | 20 | 16.2 | 14 |
| 22. | 65028 | 2006 | 15 | 18.1 | 20 | 21.4 | 26 | 25 | 23.2 | 22 | 22.2 | 22 | 15 | 11.8 |
| 23. | 65028 | 2007 | 12.8 | 13.6 | 18.3 | 22.7 | 24.4 | 23.8 | 21.5 | 20.3 | 20.5 | 17.6 | 13.3 | 10.7 |
| 24. | 65028 | 2008 | 9.5 | 14.4 | 20 | 21.2 | 23.2 | 22.8 | 21.1 | 19.5 | 19.8 | 17.5 | 13.3 | 11.5 |
| 25. | 65028 | 2009 | 11.1 | 14.2 | 19.2 | 23.4 | 24.2 | 22.4 | 22.4 | 21.1 | 22.1 | 21.5 | 14.6 | 13.6 |
| 26. | 65028 | 2010 | 14.5 | 17 | 19.7 | 23.8 | 23.7 | 23.8 | 22 | 20.7 | 21.9 | 19.6 | 14.3 | 14.1 |
| 27. | 65028 | 2011 | 13.3 | 17.9 | 17.5 | 22.3 | 24.7 | 23.8 | 20.6 | 20.5 | 21.2 | 21.2 | 16.1 | 12.2 |
| 28. | 65028 | 2012 | 12.6 | 16.4 | 18.6 | 25.4 | 26.3 | 23.4 | 21.3 | 20.4 | 21.8 | 22.1 | 19.0 | 14.6 |
| 29. | 65028 | 2013 | 30.7 | 34.3 | 39.8 | 37.8 | 38.8 | 35.6 | 32.5 | 29.9 | 32.8 | 34.9 | 34.9 | 31.1 |
| 30. | 65028 | 2014 | 30.8 | 32.2 | 37.5 | 39.7 | 37.6 | 36.6 | 33.4 | 30.7 | 32.5 | 35.9 | 34.8 | 30.7 |
| 31. | 65028 | 2015 | 28.2 | 35.1 | 36.1 | 37.5 | 40.3 | 37.4 | 33.4 | 33.1 | 32.5 | 35.9 | 33.3 | 36.1 |
| 32. | 65028 | 2016 | 28.2 | 32.5 | 38.5 | 40.5 | 39 | 35.1 | 32.2 | 30.9 | 32.3 | 36.5 | 35.5 | 30.7 |
| 33. | 65028 | 2017 | 27.8 | 31.6 | 37.5 | 39.5 | 39 | 34.7 | 31.9 | 31 | 32.9 | 35.7 | 34.1 | 30.2 |
Tushe: Hukumar Kula da Yanayi Reshen Jihar Katsina (NiMET), 2021.
Sanyi;
[gyara sashe | gyara masomin]Watan Janairu shi ne wata mafi sanyi a Katsina tare da kimanin 14.7 °C or 58.5 °F.
| S/N | Code | Shekara | Junairu | Febrelu | March | Aprelu | Mayu | Juni | Juli | Augusta | Satumba | Oktoba | Nuwamba | December |
|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
| 1. | 65028 | 1985 | 16 | 14.7 | 22.6 | 24.2 | 26.7 | 24.4 | 22.2 | 22.2 | 22.6 | 21 | 17.5 | 14.7 |
| 2. | 65028 | 1986 | 12.7 | 18 | 23.4 | 26.2 | 26.6 | 25.2 | 21.9 | 21.8 | 22.2 | 20.8 | 17.9 | 12.8 |
| 3. | 65028 | 1987 | 13.1 | 16.7 | 21.4 | 22.3 | 25.2 | 24.9 | 23.9 | 22.6 | 23.6 | 22.5 | 17.5 | 14.5 |
| 4. | 65028 | 1988 | 14.4 | 16.4 | 21.6 | 26.6 | 24.5 | 24.5 | 22.7 | 21.2 | 22.3 | 19.6 | 16.2 | 13.5 |
| 5. | 65028 | 1989 | 11.1 | 13.8 | 18.9 | 23.1 | 25.1 | 24.4 | 22.2 | 21.7 | 22.8 | 20.6 | 15.8 | 13.8 |
| 6. | 65028 | 1990 | 15.5 | 14.3 | 17 | 25.7 | 25.7 | 25.1 | 22.4 | 25.8 | 23.4 | 21 | 18.1 | 17.4 |
| 7. | 65028 | 1991 | 13.7 | 18.9 | 21.7 | 25.5 | 24.5 | 24.4 | 16.2 | 12.6 | ||||
| 8. | 65028 | 1992 | 12.5 | 13.9 | 21.9 | 24.4 | 25.1 | 23.7 | 21.4 | 21.1 | 21.6 | 20.3 | 16.5 | 12.7 |
| 9. | 65028 | 1993 | 11.3 | 15 | 19.7 | 22.7 | 24.9 | 23.1 | 21.1 | 20.7 | 21.1 | 20.5 | 17.5 | 12.5 |
| 10. | 65028 | 1994 | 12.5 | 13.5 | 19.5 | 23.7 | 24.2 | 22.1 | 20 | 19.1 | 19.6 | 20.7 | 13.5 | 10.5 |
| 11. | 65028 | 1995 | 11.2 | 13 | 19.1 | 22.7 | 23.5 | 22.2 | 20.5 | 19.4 | 19.7 | 19.8 | 14 | 12.4 |
| 12. | 65028 | 1996 | 11.4 | 14.2 | 18.7 | 20.8 | 22.3 | 20.6 | 20 | 18.8 | 19 | 18.7 | 11.8 | 12.2 |
| 13. | 65028 | 1997 | 14 | 14.1 | 21.1 | 24.7 | 24.6 | 24 | 22.9 | 22.3 | 23.1 | 23.5 | 18.9 | 14.2 |
| 14. | 65028 | 1998 | 13.7 | 17.5 | 18.6 | 25.8 | 27.7 | 24.5 | 23.1 | 21.8 | 22.3 | 21.3 | 16.9 | 13.3 |
| 15. | 65028 | 1999 | 12.6 | 16 | 20.2 | 23.1 | 24.7 | 24.1 | 20.8 | 20.4 | 20.7 | 19 | 15.1 | 11.3 |
| 16. | 65028 | 2000 | 13 | 11.2 | 16.7 | 19 | 24.3 | 23.5 | 21 | 21 | 21.9 | 19.9 | 14.1 | 11 |
| 17. | 65028 | 2001 | 20.2 | 12.6 | 16.5 | 23 | 24.6 | 23.2 | 22 | 21 | 21.9 | 19.7 | 14.6 | 12.8 |
| 18. | 65028 | 2002 | 11.7 | 13.5 | 20 | 25.6 | 26 | 24 | 22.1 | 21.9 | 22.3 | 19.8 | 13.9 | 12.8 |
| 19. | 65028 | 2003 | 16.5 | 18.6 | 24.4 | 24 | 23.6 | 23.5 | 22.2 | 22.1 | 22.5 | 19.9 | 14.5 | 12.5 |
| 20. | 65028 | 2004 | 16 | 17.5 | 25 | 25 | 24.2 | 22 | 21 | 22 | 20 | 17 | 14.7 | 12.3 |
| 21 | 65028 | 2005 | 13.4 | 19.4 | 22 | 24 | 25.2 | 24.2 | 22.7 | 21.6 | 22.3 | 20 | 16.2 | 14 |
| 22 | 65028 | 2006 | 15 | 18.1 | 20 | 21.4 | 26 | 25 | 23.2 | 22 | 22.2 | 22 | 15 | 11.8 |
| 23. | 65028 | 2007 | 12.8 | 13.6 | 18.3 | 22.7 | 24.4 | 23.8 | 21.5 | 20.3 | 20.5 | 17.6 | 13.3 | 10.7 |
| 24. | 65028 | 2008 | 9.5 | 14.4 | 20 | 21.2 | 23.2 | 22.8 | 21.1 | 19.5 | 19.8 | 17.5 | 13.3 | 11.5 |
| 25. | 65028 | 2009 | 11.1 | 14.2 | 19.2 | 23.4 | 24.2 | 22.4 | 22.4 | 21.1 | 21.1 | 21.5 | 14.6 | 13.6 |
| 26. | 65028 | 2010 | 14.5 | 17 | 19.7 | 23.8 | 23.7 | 23.8 | 22 | 20.7 | 21.9 | 19.6 | 14.3 | 14.1 |
| 27. | 65028 | 2011 | 13.3 | 17.9 | 17.5 | 22.3 | 24.7 | 23.8 | 20.6 | 20.5 | 21.2 | 21.2 | 16.1 | 12.2 |
| 28. | 65028 | 2012 | 12.6 | 16.4 | 18.6 | 25.4 | 26.3 | 23.4 | 21.3 | 20.4 | 21.8 | 22.1 | 19.0 | 14.6 |
| 29. | 65028 | 2013 | 14.3 | 15.8 | 22.1 | 23.4 | 24.3 | 22.7 | 21.9 | 21 | 22.3 | 20.9 | 18.3 | 15.9 |
| 30. | 65028 | 2014 | 14.3 | 16.7 | 21.7 | 25.8 | 25.8 | 26.7 | 24.2 | 22.1 | 22.3 | 20.7 | 18.2 | 14.2 |
| 31. | 65028 | 2015 | 12.3 | 18.1 | 20.8 | 22.2 | 26.6 | 24.8 | 22.7 | 22.3 | 23.3 | 17.6 | 13.3 | |
| 32. | 65028 | 2016 | 13.5 | 16.5 | 24.2 | 27.1 | 26.8 | 24.9 | 23.2 | 22.2 | 22 | 22.3 | 18.7 | 13.1 |
| 33. | 65028 | 2017 | 13.4 | 16.4 | 19.9 | 25 | 27.1 | 24.8 | 23.1 | 22.4 | 23.1 | 19.9 | 16.6 | 15.4 |
Tushe: Hukumar Kula da Yanayi Reshen Jihar Katsina, (NiMET) 2021
Sanannun Mutane;
[gyara sashe | gyara masomin]Hotuna
[gyara sashe | gyara masomin]-
palace of katsina
-
National museum Katsina state
-
Katsina General Hospital
-
katsina roundabout
-
Cheryl Francisconi in Katsina
-
Gidan Sarkin katsina
-
Taswirar jahar katsina
Demografi a Jihar Katsina
[gyara sashe | gyara masomin]Demografi na nufin bincike ko nazari kan yawan jama’a, rabonsu ta jinsi, shekaru, addini, harshe, da ayyukan tattalin arziki. A Jihar Katsina, demografi yana da muhimmanci wajen tsara ci gaban al’umma, ilimi, lafiya, da tsare-tsaren gwamnati.
Yawan Jama’a
[gyara sashe | gyara masomin]A cewar kididdigar hukumar ƙididdiga ta ƙasa National Population Commission (NPC), Jihar Katsina tana da fiye da 8.3 miliyan a ƙidayar shekara ta 2023, kuma ana sa ran yawan zai karu zuwa sama da 9 miliyan a cikin shekaru goma masu zuwa.
Rabe-raben Jama’a
[gyara sashe | gyara masomin]- **Maza:** kusan kashi 51%
- **Mata:** kusan kashi 49%
- **Matasa:** fiye da rabin jama’ar jihar suna ƙasa da shekaru 25, wanda ke nuna cewa Katsina tana da matasa da yawa.
- **Tsofaffi:** kashi 4–5% suna da shekaru sama da 60.
Addini
[gyara sashe | gyara masomin]Yawancin jama’ar Jihar Katsina Musulmai ne, sai kuma ƙananan kabilu masu bin Kiristanci da wasu addinai na gargajiya.
Harsuna
[gyara sashe | gyara masomin]Harshe mafi rinjaye a Katsina shi ne Hausa, amma akwai kuma Fulfulde (na Fulani), da Turanci wanda ake amfani da shi a makarantu da hukumomi.
Kabilu
[gyara sashe | gyara masomin]- Hausawa (mafi rinjaye)
- Fulani
- Gobirawa, Daurawa, Kurfayawa, da sauran ƙabilun ƙanana.
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Katsina tana da makarantu da yawa daga firamare har zuwa jami’a. Mafi shahara daga cikin su sune:
- Umaru Musa Yar’adua University (UMYU)
- Federal University Dutsin-Ma (FUDMA)
- Katsina State Polytechnic
- Makarantu da sakandire masu zaman kansu da na gwamnati da dama.
Tattalin Arziki
[gyara sashe | gyara masomin]Tattalin arzikin Katsina ya dogara ne da:
- Noma (irin su masara, gero, wake, da auduga)
- Kiwo (shanu, awaki, da tumaki)
- Sana’o’in hannu (ƙira, zane, da saka)
- Ciniki a kasuwanni kamar Dutsin-ma, Daura, da Katsina.
Matsaloli da Kalubale
[gyara sashe | gyara masomin]- Karuwar yawan jama’a ba tare da wadatattun ayyukan yi ba.
- Matsalar rashin isasshen ruwa da lafiyar muhalli.
- Kauracewar matasa zuwa manyan birane domin neman aiki.
Kammalawa
[gyara sashe | gyara masomin]Demografi a Jihar Katsina na nuna cewa jihar na da matasa da yawa, kuma tana da damar ci gaba idan aka tsara tsare-tsaren ilimi da tattalin arziki yadda ya kamata.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- National Population Commission (Nigeria)
- National Bureau of Statistics
- Rahotanni daga [[United Nations Population Fund (UNFPA)]
- ↑ Katsina (State, Nigeria) - Population Statistics, Charts, Map and Location, on March 21, 2016.
- ↑ "Umaru Musa Yar'Adua | president of Nigeria". Encyclopædia Britannica. Retrieved 2018-12-03.
- ↑ "Buhari, Katsina governor meet inside Aso Rock". Punch Newspapers. Retrieved 2018-12-03.
- ↑ "KATSINA EMIRATE COUNCIL". Retrieved 6 August 2015.
- ↑ Katsina The Encyclopædia Britannica Online. Retrieved February 20, 2007.
- ↑ 6.0 6.1 "Nigeria school attack: Hundreds of boys". BBC News. 2020-12-17. Archived from the original on 2021-02-28. Retrieved 2021-02-28.
- ↑ tabbaci gareni
- ↑ Climate Summary for Katsina.
- ↑ Yu Media Group. "Katsina, Nigeria - Detailed climate information and monthly weather forecast". Weather Atlas. Retrieved 2021-08-19.
jihar katsina tana da kananan hukuma 34