Katsina (jiha)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Jihar Katsina
Sunan Barkwancin Jiha: Jihar .
Wuri
Wurin Jihar Katsina cikin Nijeriya.
Ƙidaya
Harsuna Hausa, Fulani da Turanci
Gwamna Aminu Bello Masari (APC)
An kirkiro ta 1991
Babban Birnin Jiha Katsina
Iyaka 6,320km²
Mutane
2006 (ƙidayar Yawan Jama'a)

2,833,999
ISO 3166-2 NG-KT
fadar sarkin katsina
hoton jihar katsina kenan a wani logon lokaci
gwamnan jihar katsina Aminu Bello Masari

Jihar Katsina jiha ce daga cikin jihohin Nijeriya guda talatin da shida (36), tana yankin arewa ta yamma na kasar Nijeriya. Ansamar da ita ne daga cikin jihar Kaduna, Gwamnan Katsina a yanzu shi ne Aminu Bello Masari, wanda ya zama Gwamnan jihar ne tun bayan zabensa da akayi a shekarar 2015. Ko kafin zuwan Gwamna Aminu Bello Masari, an yi gwamnoni na soja da farar hula, kama tun daga Kanal Abdullahi Sarki Mukhtar zuwa Barista Ibrahim Shehu Shema. Mutanen jihar Katsina mafiya yawansu Hausawa ne, kuma sana'o'insu noma ne da kiwo. Daga jihar ne Shugaban kasa na yanzu wato Muhammadu Buhari ya fito da kuma tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar'adua.

daya daga cikin kofofin dake a garin katsina
kofar Laura katsina
kofar sarki Musa
Daya daga cikin manyan makarantun katsina

Jihar katsina tarihi ya nuna cewa tana da kofofi guda bakwai (7) har a yau ana amfani dasu kuma ko wace kofa tanada tarihin ta:

Kofar Marusa, Kofar ‘Yandaka, Kofar Kwaya, Kofar Kaura, Kofar Durbi, Kofar Guga, Kofar Sauri


[1]

Tarihin Kofofin Jihar Katsina[gyara sashe | Gyara masomin]

Kofar Guga kofa ce mai dunbin tarihi dake ciki birni katsina kofa ce da ke yamma maso arewacin birnin Katsina.

Daga cikin kofar, ta yi makwabtaka da unguwani dake Sararin tsako da Sullubawa dake ciki jihar katsina

Dikko sitadiyo

A wajenta kuwa, ta yi makwabtaka da Unguwarni Tudun ‘Yan Lihidda da Masallacin Idi na sarki Katsina.

Kuma wannan kofa tanan ne kofar da wani shehin malami Mai suna MUHAMMADU TANKARI yashi go ta cikin ta amma wancan lokacin sunan ta “kofar yamma” saboda itace kofar yammacin garin katsina.

Kananan hukuma[gyara sashe | Gyara masomin]

Katsina tanada kananan hukumomi guda 34 sune :-

Wannan ƙasida guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara

  1. https://www.katsinastate.gov.ng/about-katsina/history/