Sabuwa
Sabuwa | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jiha | Jihar Katsina | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 642 km² | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Sabuwa ƙaramar hukuma ce dake a Jihar Katsina, Arewa maso yammacin Nijeriya. Karamar hukumar Sabuwa ta kasance a karshen jihar katsina ta kudu maso yamma, inda kuma tayi iyaka da jihar Kadunaƙaramar .
Sannan Kuma ƙaramar Hukumar Sabuwa Tana Daya daga cikin ƙananan Hukumomi Ukku Dake ciyar da jihar Katsina Dama kasa Baki Daya ta Hanyar Noma da kiwo,
Sabuwa tanada Albarkar Fatar kasa inda yakaiga babu Wani Kalar tsiro ko Hatsi da baza'a iya Noma Dubunnan buhunanshi ba, Kabar Maganar Masara, Dawa, Wake, Shinkafa da Sauransu.
Karamar Hukumar Sabuwa Tanada Manyan Mutane da Sukayi Shura ta Bangaren Siyasa da Mulki daga Matakin Jiha Har Tarayya, Wannan Yasa Mutanen Sabuwa Sukeda Idanu a bangarori da dama.
Kasuwanci a Karamar Hukumar Sabuwa Ba Wani Abu bane mai Tasiri Musamman a Shekarun Baya, Amma yanzu Abubuwan Sun Canza Mutane sun rungumi Kasuwancin Hannu biyu Sakamakon Rashin Tsaron da Yankin yake fama dashi, Domin kuwa a yanzu Ba kowanne Yanki na Sabuwa bane ake nomawa Saboda Yan Ta'adda sun kwace Dayawan wurare, Hakan Yasa Abinci yayi karanci a wasu yankunan na Jihar Katsina Dama kasa Baki daya.
Sabuwa tayi Iyaka da Jihar Kaduna ta Bangaren Kudu da Yamma, Karamar Hukumar Giwa daga Kudu sai Karamar Hukumar Birnin Gwari daga Yamma.
Sai Karamar Hukumar Dandume Ta Jihar Katsina daga Gabas, sai Karamar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina daga Kudu.
A kidaya ta Shekarar 2006 Sabuwa Tanada yawan Jama'a da yakai 140,679 Amma a Hasashe na 2023 Sabuwa takai 251, 400.
Karuwar Bata Wuce Kashi 3.7 daga Shekarar 2006 zuwa022.
Tanada Gundumomi da yawa da Suka hada da
Sabuwa A
Sabuwa B
Machika
Damari
Gamji
Sayau
Rafin'iwa
Dugu Mu'azu
Gazari
Maibakko
✍️ Abuzarri Salisu Sabuwa
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]Abuzarri S (2023)
://nigeriadecide.org/polling_unit_category.php?state=Katsina&lga=Sabuwa
https://citypopulation.de/en/nigeria/admin/NGA021__katsina/
https://citypopulation.de/en/nigeria/admin/NGA021__katsina/