Bakori

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Globe icon.svgBakori

Wuri
 11°33′N 7°26′E / 11.55°N 7.43°E / 11.55; 7.43
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jerin jihohi a NijeriyaJihar Katsina
Labarin ƙasa
Yawan fili 679 km²
Bayanan tarihi
Ƙirƙira 1989
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Bakori karamar hukuma ce dake Jihar Katsina, Nijeriya. an kirkiri karamar hukumar a ranar 15 ga watan Mayu, shekara ta alib 1989, wanda gwamnan jihar Katsina a lokacin mulkin soja wato Major General Lawrence Onoja ya kirkire ta. Bakori na da fadin kilomita 679kmsq da yawan jama'a kimanin mutum 641,576 a kidayar shekara ta 2006. [1]Garin nada postal code 831.[2]

Tarihi[gyara sashe | Gyara masomin]

An kirkiri karamar hukumar Bakori a ranar 15 ga watan Mayu, shekara ta 1989.

Labarin Kasa[gyara sashe | Gyara masomin]

Bakori ta hada iyaka da kananan hukumomin Danja, Malumfashi, Kankara, da Funtua.

kauyukan Bakori[gyara sashe | Gyara masomin]

Akwai kauyuka da yawa a karkahin karamar hukumar Bakori, wanda suka hada da:

Barde

Kakumi

Kandurawa

Jargaba

Gazara

Dawan Musa

Kabomo

Guga

Gazara

Magaji

Tattalin Arziki[gyara sashe | Gyara masomin]

Noma shine al'amari mafi amfani ga mutanen Bakori, sukan noma masara, shinkafa, da dawa. kiwo wani abu ne mai muhimmanci a yanki wanda mafi akasarin mazajen garin makiyaya ne ko manoma. daga nan sai harkan kasuwanci wanda ke taka rawan gani wajen cigaban garin da kasuwanni kaman Kasuwar Sama.

Sanannun Mutanen Bakori[gyara sashe | Gyara masomin]

Senator Mohammad Tukur Limann - tsohon shugaban ma su rinjaye na majalisar dattawan kasa wato majority leader.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. "Bakori Local Government Area". www.manpower.com.ng. Retrieved 2021-07-12.
  2. "Post Offices- with map of LGA". NIPOST. Archived from the original on 7 October 2009. Retrieved 2009-10-20

Mahadin waje[gyara sashe | Gyara masomin]

https://web.archive.org/web/20180413051419/http://www.bakorilga.kts-ng.org/

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.