Najeriya
Najeriya | |||||
---|---|---|---|---|---|
Nijeriya (ha) Naigeria (ig) Nàìjíríà (yo) | |||||
|
|||||
| |||||
| |||||
Take | Nigeria, Muna Godiya | ||||
| |||||
Kirari |
«Unity and Faith, Peace and Progress» «Единство и вяра, мир и прогрес» «Good people, great nation» «Undod a Ffydd, Heddwch a Chynnydd» | ||||
Official symbol (en) | Costus spectabilis (en) | ||||
Suna saboda | Nijar | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Babban birni | Abuja | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 211,400,708 (2021) | ||||
• Yawan mutane | 228.85 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Bangare na | Afirka ta Yamma | ||||
Yawan fili | 923,768 km² | ||||
Wuri a ina ko kusa da wace teku | Tekun Atalanta | ||||
Wuri mafi tsayi | Chappal Waddi (2,419 m) | ||||
Wuri mafi ƙasa | Lagos Island (−0.2 m) | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Taraiyar Najeriya | ||||
Ƙirƙira | 1 Oktoba 1963 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Tsarin gwamnati | Jamhuriyar Tarayya | ||||
Majalisar zartarwa | Majalisun Najeriya | ||||
Gangar majalisa | Majalisar Taraiyar Najeriya | ||||
• Shugaban ƙasar Najeriya | Bola Ahmad Tinubu (29 Mayu 2023) | ||||
Majalisar shariar ƙoli | Kotun Koli Ta Najeriya | ||||
Ikonomi | |||||
Nominal GDP (en) | 440,833,583,992 $ (2021) | ||||
Kuɗi | Naira | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Suna ta yanar gizo | .ng (mul) | ||||
Tsarin lamba ta kiran tarho | +234 | ||||
Lambar taimakon gaggawa | *#06# da 199 (en) | ||||
Lambar ƙasa | NG | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | nigeria.gov.ng |
Najeriya (/nadʒɪəriyə/) ko Nijeriya (/niˈdʒɪəriyə/) da (turanci: Nigeria), A gwamnatance Tarayyar Najeriya, ƙasa ce da ke a Afirka ta Yamma. Tana da iyaka da kasar Nijar daga Arewa da Chadi daga Arewa, maso gabas da Kamaru daga gabas da Benin daga Yamma daga Kudanci kuma tana a gaɓar Tekun Atlantika. Jamhuriyar Tarayyar Najeriya, ta ƙunshi Jihohi guda 36, tare da babban birnin tarayya (Federal Capital Territory) Abuja inda fadar shugaban ƙasa ma'anah billahtake.[1][2][3]
Abuja tana daya daga cikin manyan birane a duniya.[4]
Najeriya ta kasance gida da dama ga 'yan asalin Turawa masu mulkin mallaka, jihohin da suka mallaka tunda (BC), tare da Nok Wayewa ta kasance ita ce karo na farko da Turawan mulkin mallaka suka fara mallakewa a Yammacin Africa a cikin karni na sha biyar (15) A zamani jihar an samo asali da Birtaniya a cikin karni na dha tara (19), yana daukar yanayin na yanzu tare da hade yankin Kudancin Najeriya da kuma kare Arewacin Najeriya a cikin shekara ta alif dubu daya da dari tara da goma sha hudu (1914), ta Lord Lugard. Ingilishi ya kafa tsarin gudanarwa da na doka yayin aiwatar da mulkin kai tsaye ta hanyar shugabannin gargajiya.[5] Najeriya, ta zama kasar tarayyar da ke da ƴanci kai tsaye a ranar 1 ga watan Oktoba, shekara ta alif dubu daya da dari tara da sittin (1960). Ta fuskanci yakin basasa daga shekara ta dubu daya da dari tara da sittin da bakwai 1967, zuwa shekarar dubu daya da dari tara da saba'in da bakwai 1970, sannan a biyo bayan zababbun gwamnatocin farar hula da mulkin kama-karya na soja, har sai an sami tabbatacciyar dimokuradiyya a shekara ta alif 1999; zaben shugaban kasa na shekara ta 2015, shi ne karo na farko da shugaban Kasa mai ci ya fadi zabensa. [6][7]
Najeriya kasa ce mai yawan Al’umma da ke zaune, sama da kabilu guda Dari, biyu da hamsin (250), wadanda ke magana da yarurruka daban daban guda 500, dukkansu suna dauke da al'adu iri daban daban. Manyan kabilun guda uku su ne Hausa – Fulani a Arewa, Yarbawa a Yamma, da kuma Igbo a gabas, wadanda suka hada da kashi 60% na yawan mutanen. Yaren hukuma shi ne Ingilishi, wanda aka zaba don saukake hadin harshe a matakin kasa. Tsarin mulkin Nijeriya ya tabbatar da ƴancin yin addini ; kuma kasa ce dake dauke da Al’ummar musulmai da Kirista, a lokaci guda. Najeriya ta kasu kashi biyu tsakanin musulmai, wadanda yawanci ke zaune a arewacin kasar, da kuma kiristoci, wadanda yawanci ke zaune a kudancin kasar, tare da ƴan tsirarun da ke yin addinin asali, kamar wadanda ke cikin kabilar Igbo da kuma yarbawa.[8][9]
Najeriya ita ce kasa mafi yawan mutane a Afirka, kuma kasa ta bakwai mafi yawan mutane a Duniya, tare da kimanin mutane miliyan 206. Tattalin arzikinta shine mafi girma a Afirka, kuma shi ne na 26, mafi girma a duniya ta hanyar GDP maras fadi, kuma na 25, mafi girma daga PPP. Najeriya galibi ana kiranta da "Giant of Africa", ma'ana karfin Afrika saboda yawan jama'a da tattalin arzikinta, kuma Bankin Duniya yana daukarta a matsayin kasuwa mai tasowa. Karamar yanki ce a cikin Afirka, matsakaiciyar karfi a cikin al'amuran kasa da kasa, sannan kuma tana daya daga cikin kasashe mafi yawan Al’umma a duniya. Koyaya, kasar tana kasa sosai a cikin jerin kasashen duniya, kuma har yanzu tana daya daga cikin kasashe masu rashawa a duniya. Najeriya memba ce ta kafuwar Tarayyar Afirka, kuma memba ce a kungiyoyin kasa da kasa da dama, wadanda suka hada da Majalisar Dinkin Duniya, kungiyar kasashen Yammacin Africa (ECOWAS), kungiyar kasashe masu arzikin man fetur, (OPEC), kuma memba na yau da kullum a gamayyar MINT, kuma tana daya daga cikin Kasashe goma sha daya masu tashen karuwan tattalin arziki wato "Next Eleven".[10]
Kirkira.
[gyara sashe | gyara masomin]
Sunan Nijeriya an dauke shi daga Kogin Neja wanda ya ratsa kasar. Wannan sunan ya samo asali ne a ranar 8, ga watan Janairun shekara ta1897, dan jaridar Ingila Flora Shaw, wanda daga baya ya auri Lord Lugard, mai kula da mulkin mallaka na Burtaniya. Nijar da ke makwabtaka da ita sun samo sunan daga wannan kogin. Asalin sunan Nijar, wanda asali ana amfani da shi ne kawai zuwa tsakiyar Kogin Neja, ba tabbas. Watakila kalmar ta canza sunan Tuareg egerew n-iger ewen da mazauna ke amfani da shi a tsakiyar kogin da ke kusa da Timbuktu kafin mulkin mallaka na Turai na karni na 19. Cite error: Closing </ref>
missing for <ref>
tag
Tarihi.
[gyara sashe | gyara masomin]Tarihi ya nuna cewar Nijeriya dadaddar kasa ce, kuma tarihi yanuna kasar na nan tun a shekara ta 500, kafin haihuwar Yesu Almasihu wato Annabi Isah (A.S), a wannan lokaci suka samata suna Kasar Hausa . Addinin musulunci ya shiga Kasar Hausa ne tun a karni na goma sha uku miladiya, a karshen karni na goma sha daya zuwa tsakiyar karni na goma sha hudu miladiya. Kanem Barno suka mamaye Kasar Hausa, kuma Fulani sun mamaye Kasar Hausa a farkon karni na goma sha tara miladiya har zuwan Turawan Mulkin Mallaka suka mamaye Lagos a shekara ta 1881 miladiya, ana cikin Yakin duniya I na farko sai Turawan Mulkin Mallaka suka karo sojojin ruwa saboda suna tsoran Jamusawa da ke Kamaru kada sumamaye Nijeriya, amma mulkin Nijeriya na farko a hannun Turawan Purtgal. A shekara ta dubu daya da dari takwas da tamanin da biyar 1885, sai Turawan Birtaniya suka mamaye duk fadin Nijeria har zuwa 01, ga oktoba, 1960. Nijeriya ta samu 'yancin kanta daga Turawan Biritaniya.
Addinai.
[gyara sashe | gyara masomin]Tsarin Mulki.
[gyara sashe | gyara masomin]A shekara ta 1966, zuwa shekara ta 1979, sojoji ne ke da ikon a kan kasar, a shekara ta 1979, a ka yi tsari wanda ya bawa talakawa ikon zaben gwamna. A shekara ta 1983, sojoji suka rushe wannan tsarin da juyin mulki har zuwa shekara ta 1998, bayan rasuwar Sani Abacha, sai aka dawo da tsarin mulki na dimokaradiya aka bawa talakawa ikon zaben shugaban da suke so, a shekara ta 1999, aka yi zabe a kasa.Obasanjo ya lashe zabe ya zama shugaban kasa na farko wanda talaka suka zaba, ya hau karo na biyu har zuwa shekara ta dubu biyu da bakwai 2007, A wannan shekara aka yi zabe, Umaru Yar'Adua ya lashe shi ne shugaban kasa a shekarar dubu biyu da sha daya 2011. Dukkansu sun fito daga jam'iyya daya ne, wato (jam'iyyar PDP).
Jihohi.
[gyara sashe | gyara masomin]Jeri | Sunan Jiha | Babban Birnin Jiha | Gwamna |
---|---|---|---|
1 | |||
2 | |||
3 | |||
4 | |||
5 | |||
6 | |||
7 | |||
8 | |||
9 | |||
10 | |||
- .Abia
- Adamawa
- Anambra
- Akwa Ibom
- Bauchi
- Bayelsa
- Benue
- Borno
- Cross River
- Delta
- Enugu
- Edo
- Ebonyi
- Ekiti
- Filato
- Gombe
- Imo
- Jigawa
- Kano
- Katsina
- Kaduna
- Kebbi
- Kogi
- Kwara
- Lagos
- Neja
- Nasarawa
- Ogun
- Osun
- Oyo
- Ondo
- Rivers
- Sokoto
- Taraba
- Yobe
- Zamfara
Babban birnin tarayya Abuja
Yarika.
[gyara sashe | gyara masomin]Manyan yarika a Najeriya sune guda uku kamar haka: Harshen Hausa da Yarbanci da Inyamuranci. Yaren Fulatanci ma yana daya daga cikin manyan yaruka a Najeriya.
-
Hausawa.
-
Shiga irin ta al'adar Hausawa.
-
Bahaushe.
-
Matsahin dan kabilar Ibo (Inyamuri) da daddare.
-
Mace da shiga iri ta matan Ibo.
-
Matan kabilar Ibo suna gudanar da biki a al'adarsu.
-
Shiga irin ta yaran kabilar Ibo.
Yarabawa sun kasance na biyu a wayanda suka fi kowa yawa a cikin kasar Najeriya, suna zaune a garuruwa irin su, Legas da Ondo da Oyo da Osun da Kwara da kuma Kogi.
-
Taron yarabawa a wani yanki a kasar yoruba , sun sanya irin na kayan su na yarbawa.
Sauran yaruka sun hada da: Fulani da Ibibio da Kanuri da Tiv da Bura da Shuwa Arab daMarghi da Kare-kare da Ɓachama da Mandara da Higgi da Kilba da Kibaku da Mafa da Glavda da Jukun da Waha da Gamargu da Igala da Nufe da Idoma da Ibibio da Efik da Anang da Ekoi da Awak da Waja da Waka.
Arzikin.
[gyara sashe | gyara masomin]Wasanni.
[gyara sashe | gyara masomin]-
Yan wasan kwallon mata na Najeriya.
-
Yan wasan Najeriya a 1978.
-
Yan Najeriya na wasan kwallon kafa.
-
Mata na wasan kwallon kafa.
-
team na wasannin mata.
-
John Mikel Obi
Fannin tsaro,
[gyara sashe | gyara masomin]Kimiya da Fasaha,
[gyara sashe | gyara masomin]Sifiri.
[gyara sashe | gyara masomin]Sifirin Jirgin Sama.
[gyara sashe | gyara masomin]Sifirin Jirgin Kasa.
[gyara sashe | gyara masomin]Al'adu.
[gyara sashe | gyara masomin]Mutane.
[gyara sashe | gyara masomin]Yaruka.
[gyara sashe | gyara masomin]Abinci.
[gyara sashe | gyara masomin]Tufafi.
[gyara sashe | gyara masomin]Ilimi.
[gyara sashe | gyara masomin]Addinai.
[gyara sashe | gyara masomin]Musulunci.
[gyara sashe | gyara masomin]Kiristanci.
[gyara sashe | gyara masomin]Hotuna.
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta.
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ http://www.unep.org/news-and-stories/story/unep-ogoniland-oil-assessment-reveals-extent-environmental-contamination-and
- ↑ https://www.greenleft.org.au/content/shell%E2%80%99s-nigeria-ecocide-creating-refugee-crisis,%20https://www.greenleft.org.au/content/shell%E2%80%99s-nigeria-ecocide-creating-refugee-crisis[permanent dead link]
- ↑ https://web.archive.org/web/20141205124719/http://www.punchng.com/news/us-sends-medical-experts-to-study-how-nigeria-contained-ebola/
- ↑ Muhammadu Buhari
- ↑ Achebe, Nwando, 1970-. The female king of colonial Nigeria : Ahebi Ugbabe. Bloomington. ISBN 978-0-253-00507-6. OCLC 707092916.CS1 maint: multiple names: authors list (link)
- ↑ https://www.theguardian.com/society/2015/may/29/outlawing-fgm-nigeria-hugely-important-precedent-say-campaigners
- ↑ "Buhari wins historic election landslide". Reuters (in Turanci). 2015-03-31. Retrieved 2020-05-25.
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/news/headlines/520849-number-of-poor-people-in-nigeria-to-reach-95-million-in-2022-world-bank.html
- ↑ https://www.washingtonpost.com/outlook/2019/09/16/official-us-poverty-rate-is-based-hopelessly-out-of-date-metric/
- ↑ https://www.fao.org/nigeria/fao-in-nigeria/nigeria-at-a-glance/en/
Ƙasashen Afirka |
Afirka ta Tsakiya | Aljeriya | Angola | Benin | Botswana | Burkina Faso | Burundi | Cabo Verde | Cadi | Côte d'Ivoire | Eritrea | eSwatini | Ethiopia | Gabon | Gambiya | Ghana | Gine | Gine Bisau | Ginen Ekweita | Jibuti | Kameru | Kenya | Komoros | Kwango (JK) | Kwango (JDK) | Laberiya | Lesotho | Libya | Madagaskar | Mali | Moris | Muritaniya | Misra | Morocco | Mozambik | Namibiya | Nijar | Nijeriya | Ruwanda | Saliyo | Sao Tome da Prinsipe | Senegal | Seychelles | Somaliya | Sudan | Sudan ta Kudu | Tanzaniya | Togo | Tunisiya | Uganda | Zambiya | Zimbabwe |
- Pages with reference errors
- Shafuka masu hade-hade
- All articles with dead external links
- Articles with dead external links from January 2024
- Articles with invalid date parameter in template
- Articles with permanently dead external links
- CS1 maint: multiple names: authors list
- CS1 Turanci-language sources (en)
- Najeriya
- Kasashen Afrika
- Pages using the Kartographer extension