Zamfara

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Zamfara
Zamfara Coat Of Arm
Map
Zamfara village
Zamfara people
Jihar Zamfara
Sunan barkwancin jiha: Noma shi ne girmanmu.
Wuri
Wurin Jihar Zamfara cikin Najeriya.
Ƙidaya
Harsuna Hausa, Fulani
Gwamna Bello Matawalle (APC)
An kirkiro ta 1996
Babban birnin jiha Gusau
Iyaka 39,762km².
Mutunci
2011 (jimilla)

3,838,160
ISO 3166-2 NG-ZA
Tambarin Gwamnan jihar Zamfara
tambarin jihar zamfara

Jihar Zamfara Jiha ce da take arewa maso yammacin ƙkasar Najeriya. Tana da yawan fili kimanin kilomita murabba’i 39,762 da yawan jama’a kimanin mutane 3,838,160 (milyan uku da dubu dari takwas da talatin da takwas da dari daya da sittin) (jimillar shekara ta 2011). Babban birnin tarayyar jahar ita ce Gusau. Bello Matawalle shi ne gwamnan jihar tun hukuncin da kotu ta yanke akan APC, shine ya bashi damar zama gwamnan ta a shekara ta 2019 har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Mahadi Ali Gusau.Dattijan jihar su ne: Janar Ali Gusau Ritaya,Ahmad Rufai Sani, Mamuda Aliyu Shinkafi, AbdulAziz Yari,Hassan Nasiha,Sahabi Liman Kaura, Mansur Dan'Ali,Kabir Garba Marafa, Dauda Lawal Dare, Hajiya Sadiya Umar Faruk da Tijjani Kaura.

Taswira Najeriya, inda jan yake nanne jihar Zamfara (Gusau)

.

Tarihin Zamfara[gyara sashe | Gyara masomin]

Asalin Zamfarawa

mutanen zamfara sun kasance maharba a lokacin baya

Zamfara ta kasance daya daga ciki masarautun asali na Hausawa. Ta kasance ana lissafata daya daga cikin Banza Bakwai wadanda ba Hausawan asali ne ba. Dalilin hakan shine, ana ganin Bare-Bari ne asalin Zamfara. Sarkin musulmi Muhammadu yana ganin Zamfarawa sun samu asali ne daga uba Bakatsine da uwa Bagobira. To su Zamfarawa sun kafa asalinsu daga Maguzawa maharba wadanda sun zauna a yankin kasar Kano kafin zuwan Bagauda tun kafin zuwan Barbushe a Dutsen Dala. Anan zamu iya fahimtar cewa Zamfarawa Hausawa ne na asali tun can azal. Zamu iya fahimtar cewa Zamfarawa dai asalinsu maharba ne daga Maguzawa. Watakila sun samu tasirin Bare- Bari a farkon tarihinsu ko kuma a ce Bare-bari na asalin sarautar Zamfara. Tarihin ƙauyen Zamfara ya samo asaline daga mutum Na farko da ya fara zama a garin, daga garin ZAMFARA wanda ake kira da BAWA. Shi yasa ake kiran garin da suna Zamfara. Farkon fadar saurautan an rusa ta. Garin ya haɗa iyakoki da Rogo sabon gari da kuma Tsohuwar Rogo ta gabas, Bari da Kaduna daga gefen yamma, Kaduna daga Kudu da Gari da Tsohuwar Rogo ta arewa.[1]

Ana ganin Zamfarawan asali wasu irin manya-manyan mutane ne, a takaice dai Samudawa ne. Dakka, sarkin Zamfara na farko kamar dai Barbushe yake, mutun ne maitsananin girma da karfi da jarumta. Akwai wasu manya- manyan kaburbura guda shida a Dutsi wadanda akace kaburburan sarakuna Zamfara ne na asali. Sabo da girman kaburburan su ana kiransu da kaburburan Samudawa. Ga alamu Zamfarawa asali na da girman jiki sosai.

Birnin Zamfara

dotsen kwatarkwashi

Zamfarawa sun fara kafa garinsu na farko ne mai suna Dutsi a kasar Zurmi ta yanzu. Don haka har yau Sarkin Zurmi na amsa sunan Sarkin Zamfara. Ance Zamfarawa saida suka kwashe shekara bakwai ba su nada sarki ba a Dutsi daga nan sai suka nada sarkinsu na farko mai suna Dakka.Don haka Sarkin Zamfara ana masa take da gimshikin gidan Dakka. Sarakuna hudu ne suka gaji Dakka a Dutsi. Daga nan sai sarauniyar Yar’Goje.

Zamfara
Zamfara road

Daga Dutsi sai Zamfarawa suka yi tafiyar kamar mil talatin akan gulbin Gagare kusa da garin Isa na yanzu suka kafa wani sabon gari mai suna Birnin Zamfara. Ance Sarkin Zamfara na bakwai mai suna Bakurukuru ya kafa birnin. Amma wasu masana tarihi sun hakikan ce cewa sarakuna ashirin da uku ne aka binne a garin Dutsi don haka ba dai sarki na bakwai ba wanda ya kafa Birnin Zamfara.Zamfarawa sun gina garinsu wanda ya habaka sosai. Sun katange shi da ganuwa.Har yanzu akwai kufan tsohon garin akwai rusashiyar ganuwa mai tsawon milyan goma-sha-uku da kofofin gari hamsin. A nan zamu iya fahimtar cewa Zamfarawa sun kafa garinsu na biyu wanda ya kasance babbar cibiyar mulkin Zamfara. Sannan garin ta samu arziƙin masarrafofin zamani irinsu Makarantun Boko, islamiyya, rijiyoyi da kuma Burtsatse da dai sauransu.[1]Ofishin siyasa ta mata an buɗeta ne a garin zamfara a shekarar 2007. [2]

Kananan hukumomi[gyara sashe | Gyara masomin]

 1. Anka
 2. Bakura
 3. Birnin-Magaji/Kiyaw
 4. Bukkuyum
 5. Bungudu
 6. Gummi
 7. Gusau
 8. Kaura-Namoda
 9. Maradun
 10. Maru
 11. Shinkafi
 12. Talata-Mafara
 13. Tsafe
 14. Zurmi

Rufe Netwok A Jihar Zamfara[gyara sashe | Gyara masomin]

A 3 ga watan satumba na shekarar 2021, gwamnatin Jihar zamfara ta bada umarnin kulle dukkan layuka da savis na daukacin Jihar zamfara gaba daya don a samu a magance matsalar tsaro. Anyi hakan ne domin yaqi da Yan bindiga Dadi da kuma Yan ta'adda. an bada umarnin rufe savis dinne na tsawon sati Biyu domin dawo da zaman lafiya da tsaro a jihar.[3].

Bibilyo[gyara sashe | Gyara masomin]

 • Kabir, Hajara Muhammad. Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4.
 • Bello, Ahmadu, Sir, 1910-1966. (1999). Alhaji Sir Ahmadu, Bello, Sardauna of Sokoto : his thoughts and vision in his own words : selected speeches and letters of the great leader. Nchi, Suleiman. Ismaila., Mohammed, Samai̕la Abdullahi. Makurdi: Oracle. ISBN 978-34637-2-1. OCLC 44137937.
 • G.karaye, Ibrahim. J. Shea, Philip. History.of karaye. ISBN 978125341


Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

 1. 1.0 1.1 G.karaye, Ibrahim. J. Shea, Philip. History of karaye. p.71 ISBN 978125341
 2. Kabir, Hajara Muhammad. Northern women development. [Nigeria]. p.164 ISBN 978-978-906-469-4.
 3. https://punchng.com/banditry-months-after-no-fly-order-fg-shuts-down-telecom-sites-in-zamfara/