Abuja
Wannan alamar launin jan shine sashin Abuja acikin taswirar Nijeriya.
- Kasa
Birnin Abuja
- Kafuwar birnin
1828
- Fadin yankin
713 km2 (275 sq mi)
- Fadin kasa
713 km2 (275 sq mi)
- Daukaka
840 m (2,760 ft)
- Yawan al'umma a shekarar (2012)
979,876
- Cunkoso
1,400/km2 (3,600/sq mi)
- Fasalin Lokaci
- Lambar akwatin gidan waya (postal code)
900211 zuwa 900288
- Shafin yanar gizo
Kanun bayannai
Abuja[gyarawa | Gyara masomin]
Abuja ne babban birnin tarayyar Nigeria. Birni ne babba mai girman gaske, birnin ya koma na tarayya ne tun a lokacin mulkin Babangida a shekarar 1991 wanda kafin lokacin tarayya a birnin Legas take. Birnin Abuja yakasance birni ne gagara-misali saboda birnin ya kunshi abubuwa da dama wanda ido ne kadai zai iya tabbatar da haka. Manyan Ma'aikatu, Makarantu, filayen jiragen sama, stadium da dai sauran manyan-manyan ma'aikatun gwamnati wanda suke juya akalar kasar baki daya. Acikin birnin Abuja akwai mutane akalla 776,298 a kidayar shekarar 2006, kasancewar birnin na tarayya [1] ne wato ya tara duk jinsin mutane da kabilun dake Nijeriya gaba daya, kowacce jiha a Nijeriya tanada wakilai a sassa daban-daban a cikin Abuja domin ganin sun wakilci jiharsu a fage da dama na ciyar da jiharsu gaba. Acikin birnin Abuja akwai wuraren shakatawa da dama ko wuraren bude ido musamman ga baki, wadanda suke muradin kashe kwarkwatar ido ta fagen kallon abubuwan ban al'ajabi, da debe kewa.
Manyan wurare a Abuja[gyarawa | Gyara masomin]
- Gidan gwamnati (Villa)
- Majalisar Dattawa
- Majalisar Wakilai (NASS)
- Babban kotun koli (supreme court)
- Babban Bankin Nigeria (CBN)
- Babban ofishin sojoji
- Babban ofishin yan sanda na kasa
- Ma'aikatar sufuri ta kasa
- Babban ofishin kwastam na kasa
- Ofishin gamayyar Afrika (ECOWAS)
Chanjin yanayi a sashen Abuja[gyarawa | Gyara masomin]
Ruwan sama a Abuja yana farawa ne daga watan Aprilu sannan ya kare a watan October, a yayin da zafin hasken rana yake kaiwa makin 28 °C (82.4 °F) zuwa 30 °C (86.0 °F) sannan kuma sanyin dare a maki mafi karanci yana kaiwa 22 °C (71.6 °F) zuwa 23 °C (73.4 °F). Amma a lokacin rani, zafin hasken rana a bisa maki mafi girma yana kaiwa 40 °C (104.0 °F) amma yanayin yana sauki da dare akan makin ma'aunin celcius 12 °C (53.6 °F). har zuwa karshen dare yana kaiwa 30 °C (86.0 °F). wannan shine adadin makin sauyin yanayi da sashin birni Abuja ke fuskata a takaice.
Tashoshin Gidan Radio a yankin Abuja
- 88.9 - Brila FM (Abuja) - sports
- 92.1 - Vision FM
- 92.9 - Kapital FM
- 93.5 - ASO Radio
- 94.7 - Rhythm FM (Abuja)
- 96.9 - Cool FM (Abuja)
- 98.3 - Hot FM (Abuja)
- 99.5 - Wazobia FM (Abuja)
- 99.9 - Kiss FM (Abuja)
- 100.5 - RayPower FM (Abuja)
- 104 - Love FM (Abuja)
- 95.1 - Nigeria Info
- 106 - WE FM
'
SASSAN ABUJA (Districts) [2]
Abuja tana da sassa wato (districts) da dama tun daga Phase 1 har zuwa phase 3 sune kamar haka:
SASSA NA PHASE 1[gyarawa | Gyara masomin]
- Central cadastral zone A00
- Garki I District cadastral zone A01
- Wuse 1 District cadastral zone A02
- Garki II District cadastral zone A03
- Asokoro cadastral zone A04
- Maitama Districts cadastral zone A05
- Maitama cadastral zone A06
- Wuse II District cadastral zone A07
- Wuse II cadastral zone A08
- Guzape District zone A09
SASSA NA PHASE 2[gyarawa | Gyara masomin]
- kukwuaba cadastral zone B00
- Gudu cadastral zone B01
- Durumi cadastral zone B02
- Wuye cadastral zone B03
- Jabi cadastral zone B04
- Utako cadastral zone B05
- Mabushi cadastral zone B06
- Jahi cadastral zone B08
- Kado cadastral zone B09
- Dakibiyu cadastral zone B10
- Kaura cadastral zone B11
- Duboyi cadastral zone B12
- Gaduwa cadastral zone B13
- Dutse cadastral zone B14
- Katampe Ext cadastral zone B19
SASSA NA PHASE 3[gyarawa | Gyara masomin]
- Institution and Research Cadastral Zone C00,
- Karmo Cadastral Zone C01,
- Gwarimpa Cadastral Zone C02.
- Dape Cadastral Zone C04,
- Kafe Cadastral Zone C05
- Nbora Cadastral Zone C06,
- Galadimawa Cadastral Zone C07,
- Dakwo Cadastral Zone C08,
- Lokogoma Cadastral Zone C09,
- Wumba Cadastral Zone C10,
- Idu Industrial Cadastral Zone C16
- ↑ "Tarihin kafuwar Najeriya tun shekaru aru-aru" http://www.bbc.co.uk/hausa/news/2010/09/100914_early_history_nigeria50.shtml
- ↑ [[http://abuja-ng.com/contactus.html